Falalar : La'ilaha Illal Lahu

Falalar : La'ilaha Illal Lahu

Falalar : La’ilaha Illal Lahu”

Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “An gina musulunci a bisa abubuwa biyar, shaidawa babu bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad Manzon Allah, da tsaida sallah, da bayar da zakka, da hajji, da azumin watar Ramadan” (Bukhari ne ya rawaito shi)

Kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Mafi alherin abin na faxa ni da Annabawan da suke gabanina, shi ne “Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai, ba shi da abokin tarayya, mulki da godiya sun tabbata gare shi, kuma shi mai iko ne akan komai” (Tirmizi ne ya rawaito shi)

Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Haqiqa Annabin Allah Nuhu lokacin da mutuwa ta zo masa, ya cewa xansa, “Ina umartarka da La’ilaha Illal Lahu, domin da a ce sammai bakwai da qasa bakwai za a sanya su a hannun ma’auni xaya, a xora La’ilaha Illal Lahu a xaya hannun, da la’ilaha Illal Lahu ta runjaye shi. Da a ce sammai bakwai da qasa bakwai sun haxe sun zama dunqulallen abu xaya, da la’ilaha Illal lahu da rinjaye su”. (Bukhari ne ya rawaito shi a cikin Al’adabul Mufrad).

Sharuxxan La’ilaha Illal Lahu

Saboda La’ilaha Illal Lahu aka qawata Aljannah, aka rura wuta, aka tsayar da kasuwar kyawawan ayyuka da munana.

1-Sanin Ma’anarta: Shi ne wanda ya faxe ta ya san ma’anar wannan kalma, da abin da ta qunsa na kore bauta ga wanin Allah, da tabbatar da ita ga Allah mai girma da buwaya. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Ka sani babu abin bautawa da gaskiya sai Allah” (Muhammad : 19)

2-Sakankancewa (Yaqini): Shi ne kada mai faxinta ya yi shakka a cikinka, ko cikin abin da ta qunsa, saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki “kaxai muminai sune waxanda suka yi imani da Allah da Manzonsa, sannan ba su yi shakka ba, suka yi jihadi da dukiyoyinsu da rayukansu a kan tafarkin Allah, waxannan su ne masu gaskiya” (Alhujurat : 15)

Kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “(Kalmar Shahada) na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Manzon Allah ne. Bawa ba zai gamu da Allah da su ba, ba ya shakka a cikinsu face sai ya shiga Aljannah”. (Muslim ne ya rawaito shi)

3-Karvar abin da kalmar ta hukuntar a cikin zuciya da harshe: Abin da ake nufi da karva shi kishiyar mayarwa da qin yarda da girman kai. Allah mai girma da buwaya ya ce, “Haka muke aikatawa masu laifi. Sun kasance idan an ce da su, babu abin da bautawa da gaskiya suna yin girman kai” (Assaafat : 34 – 35)

Cikakkiyar bauta ita ce bautar da zuciya. Duk abin da ya bautar da zuciya, to zuciyar ta zama baiwarsa.

4-Miqa wuya zuwa ga abin da ta nuna: Wato bawa ya zama yana aiki da abin da Allah ya yi umarni da shi a cikin wannan kalma, yana barin abin da ta hana. Allah mai girma da buwaya ya ce, “Wanda duk ya fuskantar da fuskarsa zuwa ga Allah yana mai kyautatawa, to ya yi riqo da igiya mai qarfi. Sannan ga Allah ne makomar al’amura suke” (Luqman : 22)

5-Gaskiya: Ma’anarta mai faxar wannan kalma ya faxe ta yana mai gaskiya a cikin zuciyarsa, zuciyarsa da harshensa su dace akan abin. Allah ya ce, “Daga cikin mutane akwai wanda yake cewa mun yi imani da Allah da ranar qarshe, amma fa ba muminai ne ba. Suna yaudarar Allah da waxanda suka yi imani, amma ba kowa suke yaudara ba sai kawunansu sai dai ba su sani ba” (Albaqra : 8 – 9)

6-Ikhlasi : Shi ne nufatar Allah mai girma da buwaya wajen faxin wannan kalma. Allah ya ce, “Ba a umarce su ba, sai dai su bautawa Allah suna masu tsantsanta addini gare shi, su tsayar da sallah su ba da zakkah, wannan shi ne addinin hanya miqaqqiya”. (Albayyinah : 5)

7-Son wannan kalma da ma’abotanta, masu aiki da ita, waxanda suka lazimce ta da sharuxxanta, da qin abin da ya warwareta, Allah mai girma da buwaya ya ce, “Daga cikin mutane akwai waxanda suke riqon wasu kishiyoyi koma bayan Allah, suna son su kamar yadda suke son Allah. Waxanda suka yi imani sun fi tsananin son Allah”. (Albaqra : 165)

Duk lokacin da zuciya ta qara son Allah, sai ta qara bauta masa, ta kuma ‘yantu daga waninsa

Wannan shi ne ma’anar “La’ilaha Illal lahu” kuma waxannan su ne sharuxxanta, waxanda da su ne take zama sababin tsira a wajen Allah. An cewa Alhasanul Basariy : wasu mutane suna cewa, wanda ya ce La’ilaha Illal Lahu, sai shiga Aljannah, zai Alhasan ya ce, “Wanda ya ce la’ilaha illal Lahu, ya bayar da haqqinta da farillarta to zai shiga Aljannah.

Kalmar La’ilaha illal Lahu ba ta amfanar mai faxarta sai ya zama mai aiki da ita, wanda ya zo da sharuxxanta. Amma duk wanda ya faxeta kuma ya bar aiki da abin da ta nuna, to faxinta ba zai amfane shi ba, har sai ya haxa magana da aiki.

Abubuwan da suke warware la’ilaha Illal Lahu

1-Haxa Allah da wani : Abin da ake nufi a nan shi ne :Babbar shirka, wadda take fitar da mutum daga addini, kuma Allah baya gafarta wanda ya mutu a cikinta. Ita ce sanya wa Allah abokin tarayya a cikin haqqinsa na bauta da ayyuka, da sunayensa da sifofinsa. Allah mai girma da buwaya ya ce, “Haqiqa Allah ba ya gafarta wa a yi shirka da shi, amma yana gafarta abin da yake koma bayan hakan, ga wanda ya ga dama. Duk wanda ya yi shirka da Allah to ya vata vata mai nisa” (Annisa’i : 116)

Ba ya hallata wani ya kira Allah da wani suna sai da sunayensa mafiya kyau. Kiran da aka yi umarni da shi, shi ne wanda faxin Allah Maxaukakin Sarki ya nuna, inda ya ce, “Allah yana da sunaye mafiya kyau, ku bauta msa da su. Ku qyale waxanda suke karkacewa a cikin sunayensa, za a saka musu abin da suka kasance suna aikatawa”.(Al’aaraf : 180)

Imam Abu Hanifa

Kuma Allah ya ce, “An yi maka wahayi da waxanda suke gabaninka cewa wallahi idan ka yi shirka ayyukanka za su rushe, kuma wallahi za ka kasance a cikin hasararru. Allah kaxai ka bauta masa ka kasance a cikin masu godiya”. (Azzumar : 65 – 66)

2-Wanda ya sanya wasu tsani tsakaninsa da Allah, yana bauta musu, yana neman cetonsu, yana dogara a kansu, yana kusantarsu da ibada, to duk wanda ya yi haka, ya warware la’ilaha Illal Lahu.

3-Duk wanda bai kafirta arna ba (Mushirikai) ko kuma ya yi shakka akan kafircinsu, ko kuma ya inganta hanyarsu, saboda hakan yana nuna yana shakka akan abin da yake kai na musulunci, wanda Allah bai yarda da wani addini wanda ba shi ba. To duk wanda ya yi shakka akan kafircin wanda ya bautawa wanin Allah, ko ya kawar da wani abu na ibada zuwa ga wanin Allah, ko kuma ya yi shakkar kafircin Yahudu da Nasara da maguzawa, ko ya yi shakkar cewa suna cikin wuta, ko ya inganta wani abu na hanyoyin mushirikai arna ko ayyukansu waxanda nassi ya zo a kai cewa kafirce ni, to wannan mutum ya kafirta.

4-Wanda ya qudurce cewa wata shiriya wadda ba ta Annabi (S.A.W) ba ta fi cika akan shiriyar Annabi, hakama hukuncin wani wanda ba Annabi ba, ya fi na Annabi (S.A.W) kyau, to ya kafirta, kamar wanda zai fifita dokokin qabila ko na al’ada a kan shari’ar musulunci, ko kuma ya halatta yin hukunci da su, ko kuma ya ce daidai suke da shari’ar musulunci, to duk wannan kafircewa Allah mai girma ne, Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Duk Waxanda ba su yi hukunci da abin da Allah ya saukar ba, to waxannan su ne kafirai” (Al’ma’idah : 44)

Da faxinsa : “Na rantse da Ubangijinka ba za su yi imani ba, har sai sun kai maka hukuncin abin da ya faru tsakaninsu, sannan baza su ji wata damuwa ba akan abin da ka hukunta, sannan su sallama sallamawa” (Annisa’i : 65)

5-Wanda duk ya qi wani abi daga abin da Manzon Allah (S.A.W) ya zo da shi, koda ya yi aiki da abin. Kamar wanda zai qi sallah, To ya zama kafiri, koda kuwa ya yi aiki da ita, don bai so abin da Allah ya yi umarni da shi ba, kuma daga cikin sharuxxan La’ilaha Illal Lahu son abin da ta zo da shi daga Allah, duk kuwa wanda ya qi abin da Manzon Allah (S.A.W) ya zo da shi, to bai tabbatar da ma’anar shaidawa da yi Muhammad Manzon Allah ne ba, don abin da take nunawa shi ne sallamawa abin da ya zo da shi, a cikin jin daxi da kwanciyar hankali.

6-Duk wanda ya yi izgili da wani abu daga addinin Allah, ko wani lada ko uquba da Allah ya ce zai yi, to ya zama kafiri, saboda bai girmama wannan addinin ba, wanda ya wajaba a girmama shi da girmama abin da ya zo da shi, saboda Allah ya yanke hukuncin kafirci akan wasu mutane da suke muminai saboda sun yi wa Manzon Allah da Sahabbansa izgili, inda suka ce, “Mu ba mu tava ganin irin waxannan makarantar namu, masu kwaxayi, masu qarya, matsorata a wurin yaqi, sai Allah ya saukar da : “Idan ka tambaye su, tabbas za su ce, mu fa muna kutsawa ne muna wasa. Ka ce, yanzu da Allah da ayoyinsa da manzonsa kuke wa Izgizanci. To kada ku kawo wani hanzari, kun kafirta bayan imaninku” (Attaubah : 65 – 66)

Allah ya yanke hukuncin da kafircinsu duk da cewa kafin haka su muminai ne, Kuma shi ne Abin da faxin Allah yake nunawa : “Kun kafirta bayan imaninku” (Attaubah : 66)

Sai Allah ya tabbatar musu da imani kafin su faxi abin da suka faxa, sannan ya kafirta su, duk da cewa sun faxi abin da suka faxa a wasa da raha, don su yanke wahalar tafiya da wannan zancen.

7-Sihiri da tsafi: Shi ne wasu layu da tofi da qulli da suke yin tasiri a kan zuciya da jiki, suna kaiwa zuwa ga kisa da raba tsakanin mutum da matarsa, wannan kafirci ne. Allah mai girma da buwaya ya ce, “Kuma alhali haqiqa sun sani duk wanda ya saye shi (Sihiri) ba shi da wani rabo a lahira” (Albaqra : 102)

Abin da ake nufi, bai da wani rabo ko kaxan. Gabanin nan Allah ya ce, “Ba sa koyawa kowa har sai sun ce masa, mu fitina ne kada ka kafirta” (Albaqra : 102)

Kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa, suka ce, waxanne ne su ya Manzon Allah, sai ya ce, “Shirka da Allah, da Sihiri, da kashe ran da Allah ya haramta sai dai da gaskiya, da cin riba, da cin dukiyar maraya, da juya baya rana yaqi, da yiwa katangaggu mata kamammu muminai qazafi” (Bukhari ne ya rawaito shi)

Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Duk wanda ya yi wani qulli, sannan ya yi tofi a cikinsa, to ya yi sihiri, wanda ya yi sihiri kuwa to ya yi shirka, wanda ya rataya wani abu za a bar shi da shi” (Nasa’i ne ya rawaito shi)

Yana cikin sihiri amfani da taurari da falakai don gano wasu abubuwan da za su faru a bayan qasa, saboda hadisin da Abu Dawud ya rawaito daga Abdullahi xan Abbas, Manzon Allah (S.A.W) ya ce,“Wanda duk ya xosani wani abu daga ilimin taurari, to ya xosani wani yanki na sihiri, yana qarawa sihirinsa yana qaruwa” (Baihaqi ne ya rawaito shi)

Allah mai girma da buwaya ya ce, “Mai sihiri ba ya cin nasara duk da inda ya vullo” (Xaha : 69)

Yana cikin sihiri kawar da masoya da raba su da junansu, da qulla soyayyarsu ga wasu daban.

Ilimi mai amfani shi ne wanda ya kai bawa zuwa ga kaxaita Allah (Tauhidi) da abin da ya biyo baya na hidimar mutane da kyautata musu. Ilimi maras amfani shi ne ilimin da ya kai mutum zuwa ga shirka da Allah da cutar da xan Adam.

8-Taimakon Arna (mushirikai) da ba su goyon baya don karya musulmi. Shi ne jivintar da Allah ya faxa a kansu inda ya ce, “Duk wanda ya jivince su daga cikinku to shi ma yana cikinsu”. (Alma’idah : 51)

Jivinta a nan, ba a nufin so da qawance da karkata gare su ba, wannan babban zunubi ne bai kai kafirci ba, Jivintar da ake nufi a nan ita ce taimakon kafirai don karya musulmai, da shirya wa musulmai makirci tare da su, kamar dai yadda munafukai suke. Mai jivintar arna akan lamarin duniya yana kan haxari mai girma

9-Wanda duk yake ganin wani yana da damar barin shari’ar Muhammad (S.A.W) to ya kafirta, saboda shari’ar musulunci wadda Allah ya aiko Annabi Muhammad (S.A.W) da ita, ta mamaye dukkan shari’u kuma ta shafe su, Allah ba ya karvar komai sai musulunci, Allah ya ce, “Haqiqa addini a wurin Allah shi ne musulunci” (Ali-Imran : 19)

Ya sake cewa, “Wanda ya nemi wani addini ba musulunci ba, to ba za a karva daga gare shi ba, kuma a lahira yana cikin hasararru” (Al-Imran : 85)

Ya ce, “Ka ce, in kun kasance kuna son Allah to ku bi ni, Allah zai so ku, ya gafarta muku zunubanku, Allah mai gafara ne mai jinqai. Ka ce, ku bi Allah da Manzonsa, idan kun ba da baya to Allah ba ya son kafirai” (Al-Imran : 31 – 32)

Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Na rantse da wanda ran Muhammad yake hannunsa, babu wani wanda zai ji labarina a cikin wannan al’umma, bayahude ne ko kirista, sannan bai yi imani da abin da aka aiko ni da shi ba, face sai ya kasance cikin ‘yan wuta” (Muslim ne ya rawaito shi)

Zuciya idan ba ta fuskanci Allah ba, ba ta bijirewa waninsa ba, to ta zama mai shirka da Allah.

Daga misalin irin wannan abu, abin da jahilai suke rayawa na fitar waliyyai daga biyayyar Manzon Allah Muhammad (S.A.W), wannan kuwa shi ne haqiqanin kafirci da fita daga musulunci.

10-Wanda ya bijirewa addinin Allah gabaxayansa, ba ya aiki da shi, to ya zama kafiri. Duk wanda ya bijirewa aiki gabaxaya, ya wadatu da abin da yake kai na kafirci, idan an kira shi zuwa ga musulunci sai ya bijire, ya qi, ko kuma idan ya san (addini) sai ya bijire ya qi aiki da shi ba, ya qi karva, to wannan ya zama kafiri.

Ilimi kamar wata bishiya ce mai ‘ya ‘ya, da take fitar da halaye kyawawa, da aiki na gari, da kyakkyawar kama. Jahilci kuwa wata bishiya ce da take fitar da munanan halaye, da mummunar kama.

Waxannan abubuwan da suke warware musulunci babu bambanci wajen aikata su, ga wanda ya yi su da gaske, ko da wasa, ko tsoro, matuqar dai sun yi su da sani, kuma da gangan. Sai dai wanda aka tilasta tilastawa da dole, to sai ya amsawa waxanda suka tilasta shi da harshe, saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Sai wanda aka tilasta alhali zuciyarsa tana cike da imani. Amma wanda ya zuciyarsa ta nutsu da kafirci..” (Annahl : 106)

Duk wanda aka tilasta aka ya yi kafirci, sai ya yi kafircin yana mai yarda da shi, to wannan ya kafirta. Amma wanda ya aikata kafircin don ya kawar da haxarin mutuwa daga kansa, zuciyarsa kuma tana cike da nutsuwa da Imani to wannan ya kuvuta, babu komai a kansa, saboda faxin Allah mai girma da buwaya, “Sai dai in kun kare kanku daga gare su karewa”. (Al-Imaran : 28)



Tags: