Ya wanda yake ji, ka saurari addu’o’inmu, ka amsa mana, kai ne mai ganin ayyukanmu, da gazawarmu da buqatunmu, kai kaxai.
Yana jin muryoyi dukkansu, masu rauni da masu qarfi, wata muryar ba ta hana shi ya ji wata, wani mai roqo baya ha na shi jin wani mai roqon.
“Mai ji mai gani”.. Yana jin maganarka, don haka ka yi wa kanka hisabi, yana jin addu’arka, don haka ka nace masa, yana ganin ayyukanka, kada ka voye masa komai, ka kyautata, Allah yana son masu kyautatawa.Yana ganin komai, duk qanqantarsa ko girmansa, ko voyayye ciki dare ko rana.
Yana jin magana, duk da savanin yaruka, da buqatu kala-kala
Yana ganin tafiyar baqar tururuwa a cikin duhun dare, a kan kurman dutse. Yana ganin abin da yake qasan bakwai, kamar yadda yake ganin abin da yake saman bakwai.
Babu wani abin da yake voye masa, babu wani abin da yake guje masa.