Wanda ya isarwa da dukkan halittu abincinsu, ya halitta musu abin da za su rayu da shi, ya ba su abin da za su sha ya qosar da su, ya ba su rayuwa mai kyau.
Wanda yake ciyar da zukata da ilimi kala-kala, ta rayu da shi, hankula su kwanta da shi.
Ya Allah wanda yake tsaye da sha’anin bayi, da jujjuya rayuwarsu da makomarsu, kiyayewarka da afuwarka da lafiyarka muke nema.. “Allah ya kasance mai kiyayewa akan dukkan komai” (Annisa’i : 85)