Cikakke a sunayensa da siffofinsa, ba wata tawaya ko gazawa dake samunsa
“Wanda ake nufa da buqata”.. Wanda halittu gabaxayansu suke nufa da dukkan buqatunsu da lalurorinsu da halayensu, saboda kamalar cikarsa, a zatinsa da sunayensa da siffofinsa da ayyukansa.Mawadacin da kowa yake buqatarsa, shi kuma ba ya buqatar kowa.. “yana ciyarwa shi kuma ba a ciyar da shi” (Al-an’am : 14)
Ubangiji mai jujjuya al’amura, mai mulki, mai tasrifi.
Zukata sun fuskance shi da buqatu, ya ba su bai hana su ba, sun kirawo shi akan buqatunsu, ya yaye musu damuwa ya amsa musu. Waxanda suka bar shi sun kirawo shi ya ba su, waxanda suke jin tsoro sun koma wajensa ya amintar da su, masu tauhidi sun yi fata a wajensa, ya ba su abin da suka yi fata, waxanda suke cikin musiba sun kirawo shi, ya kuvutar da su, dukkan bayi sun sunkuyar da kai gare shi.