Allah mabuwayi mai qarfi mai rinjaye.
Wanda qarfin mai qarfi ba ya cutar da shi, kuma ikon mai iko ba ya gajiyar da shi, albarkarsa ta yawaita maxaukaki masani.
“Mabuwayi”.. Wanda yake da buwaya gabaxaya, buwayar qarfi, buwayar rinjaye, buwayar kariya, babu wanda zai iya cutar da shi daga halittunsa, ya rinjayi dukkan halitta, kuma sun sunkuyar da kai gare shi, saboda girmansa.Buwayarsa ta cika, kowa da kowa ya sunkuyar da kai gare shi, duk wani mai qarfi ya yi rauni a gabansa, duk wanda ba shi ba qasqantacce ne, duk wani mahluki na qasqanta ne a gurinsa.
Yana ba wanda ya ga dama buwaya, yana qwaceta daga wanda ya ga dama, yana qasqanta wanda ya ga dama, a hannunsa alheri yake, Allah ya ce, “Haqiqa buwaya gabaxayanta ta Allah ce” (Yunus : 65)
Babu wata xaukaka ta nasaba ko matsayi ko dukiya, sai daga wajensa kuma daga gare shi.
Ba wanda yake xaukaka sai da xaukakarsa, ba mai qarfi sai da falalarsa, duk wanda zai fake ya fake da shi, duk wanda yake neman xaukaka to ya fuskanci Allah da zuciyarsa... “Xaukaka ta Allah ce da Manzonsa da Muminai” (Almunafiqun : 8)