Kamar yadda tasirin aikin kaxaita Allah (Tauhidi) ya bayyana a cikin zuciyar mumini, da halayensa, haka nan ma yake bayyana xabi’unsa tare da mutane. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Kaxai an aiko ni don in cika kyawawan halaye” (Baihaqi ne ya rawaito shi)
Kai Manzon Allah (S.A.W) ya haxa tsakanin imani da halaye na qwarai, ya ce, “Mafi cikar muminai imani shi ne wanda ya fisu kyawawan halaye, da tausasawa iyalansa” (Tirmizi ne ya rawaito shi)
Musulmi mai tauhidi yana hararo kulawar Allah gare shi, da yadda Allah yake kiyaye bayinsa, yake tausaya musu a cikin dukkan bangarorin rayuwa gabaxaya.
1-Mu’amala da iyaye :
Musulmi mai kaxaita Allah ya fi kowa kula da haqqin iyayen shi. Allah Maxaukakin Sarki ya haxa haqqinsa da haqqin iyaye a cikin littafinsa, inda ya ce, “Ubangijinka ya hukunta cewa kada ku bautawa kowa sai shi, iyaye kuma a kyautata musu. Idan xayansu ya girma a wajenka ko su duka biyun, to kada ka ce musu tir, kada ka yi musu tsawa, ka faxa musu magana ta girmamawa. Ka sunkuyar musu da fikafikan rahama, ka ce :Ubangiji ka jiqansu kamar yadda suka rene ni ina qarami. Ubangijinku yafi ku sanin abin da yake zukatanku, in kun kasance na qwarai to shi Allah mai gafara ne ga masu komawa wajensa”. (Al-isra’i : 23 – 25).
Kuma Allah yana cewa, “Mun yi wa mutum wasiyya da iyayansa ya kyautata musu. Idan matsa maka a kan ka yi shirka da ni a cikin abin da ba ka da ilimi, ka da ka yi musu biyayya, gareni makomarku take, sannan in ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa” (Al’ankabut : 8)
2-Mu’amala Da ‘Ya’ya :
Duk da cewa ‘ya’ya su ne adon duniya, Allah yana cewa game da su : “Dukiya da ‘ya’ya adon duniya ne” (Alkahfi : 46)
Sai dai tauhidin da yake cikin zuciyar mumini yana kiran shi zuwa ga yi wa ‘ya’yansa tarbiyya. Allah ya kira muminai da sunansu na imani, zuwa ga kare kawunansu da iyalansu daga wutar Jahannama, Allah ya ce, “Ya ku waxanda suka yi imani, ku kiyaye kanku da iyalanku daga wata wuta, wadda makamashinta mutane ne da duwatsu, a kanta akwai wasu Mala’iku masu tsauri da tsanani, ba sa savawa Allah cikin abin da ya umarce su, suna kuma aikata abin da ya umarce su”. (Attahrim : 6)
Ya sanya tarbiyya nauyi ne akan dukkan wanda yake kiwo, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Dukkaninku masu kiwo ne, kuma kowannenku abin tambaya ne a kan abin kiwonsa, shugaba mai kiwo ne, kuma abin tambaya ne akan abin kiwonsa, mutum mai kiwo ne a cikin iyalansa, shi ma abin tambaya ne akan abin kiwonsa, mace ma mai kiwo ce a gidan mijinta, kuma abar tambaya ce akan abin kiwonta, mai hidima ma mai kiwo ne, kuma abin tambaya ne akan abin kiwonsa” (Bukhari ne ua rawaito shi)
3-Mu’amala Da Mata :
Musulmi mai tauhidi yana kiyaye haqqin matarsa, yana kula da tsoron Allah wajen kiyaye haqqoqinta da kyautata mata. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Su ma mata suna da irin abin da yake kansu na kyautatawa” (Albaqra : 228)
Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Mafificinku, shi ne mafi kyautatawa ga iyalansa, ni kuma nine mafi kyautatawarku ga iyalaina”. (Tirmizi ne ya rawaito shi)
Lokacin da mata suka zo wajen Manzon Allah (S.A.W) suna kawo kukan mazajensu, sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce da su : “Zavavvunku su ne zavavvunku a wurin matansu” (Ibnu Majah ne ya rawaito shi)
4-Mu’amala Da Miji :
Tauhidi yana haifar wa da mace mumina tsoron Allah, har ta zama mai tsoron Allah da kula da haqqin mjinta, don ta samu Aljannah. Manzon Allah (S.A.W) ya ce : “Idan mace ta sallaci sallolinta biyar, ta yi azumin watan Ramadan, ta kiyaye farjinta, ta yi wa mijinta biyayya. To za a ce da ita “Ki shiga Aljannah daga duk qofar da kika ga dama” (Ahmad ne ya rawaito shi)
Allah ya umarce ta ka da ta xora wa mijinta abin da ba zai iya ba. Allah Ta’ala ya ce, “Don mai yalwa ya ciyar daga yalwarsa, wanda kuma aka quntata masa arzikinsa to ya ciyar daga abin da Allah ya ba shi. Ba ma xora wa rai sai abin da muka ba ta. Allah Zai sanya sauqi bayan tsanani” (Axxalaq : 7)
Ka da ta ce ya sake ta, saboda Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Duk matar da ta tambayi mijinta saki, ba tare da wani laifi ba, to Aljannah ta zama haramun a gare ta” (Ahmad ne ya rawaito shi)
Sada zumunci da kiyaye haqqin maqota : Allah Maxaukakin Sarki ya haxa ibadarsa da tsarkake shi shi kaxai, da mu’amalar mutum tare da danginsa da makusantansa da maqotansa. Allah Ta’ala ya ce, “Ku bautawa Allah ka da ku yi shirka da shi da wani abu. Iyaye kuma ku kyautata musu, da Makusanta, da Marayu, da Miskinai, da Maqoci na kusa, da Maqoci na nesa, da wanda yake kusa (mata) da matafiyi da abin da damanku ta mallaka (bayinku). Haqiqa Allah ba ya son mai alfari da taqama”(Annisa’i : 36)
Kuma Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Ka ba wa makusanci haqqinsa da miskini da matafiya. Wannan shi ne alheri ga waxanda suke nufin fuskar Allah. Kuma waxannan su ne masu rabo” (Arruum : 38)
Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Wanda ya yi imani da Allah da ranar lahiri, to ya kyautatawa maqocinsa” (Muslim ne ya rawaito shi)
Imani yana haifar da kyatatawa mutane, da yi musu nasiha, da mu’amalar gaskiya tare da su. Waxannan kuwa su ne mafi falalar ayyukan da mumini yake kusantar Allah da su.
1-Kyawawan Halaye :
Allah ya siffata Annabinsa (S.A.W) ya ce, “Haqiqa kai kana kan halaye masu girma” (Alqalam : 4)
Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Mafi yawancin abin da yake shigar da mutane Aljannah shi ne tsoron Allah da kyawawan halaye” (Tirmizi ne ya rawaito shi)
Kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Wanda Allah ya fi so a cikin mutane, shi ne wanda ya fi amfanar mutane. Aikin da Allah ya fi so, shi ne farin ciki da zaka sa musulmi, ko ka yaye masa wata damuwa, ko ka biya masa bashi Ko ka kore masa yunwa. In shiga wata buqata da xan uwana ya fi soyuwa a wurina a kan in yi I’tikafin wata guda a masallacin Madinah” (Xabarani ne ya rawaito shi)
Ba zai yi wu ba, a ce Manzon Allah (S.A.W) ya koyar da al’ummarsa tsarki, amma kuma bai koya musu tauhidi ba. Tauhidi shi ne abin da Manzon Allah (S.A.W) yake cewa : “An umarce ni in yaqi mutane, har sai sun ce “La’ilah Illal Lahu” (Bukhari ne ya rawaito shi) abin da aka kare dukiya da jini da shi shi ne tauhidi.2-Gaskiya :
Allah Ta’ala ya ce, “Ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah, ku zama tare da masu gaskiya”. (Attaubah : 119)
Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Haqiqa gaskiya tana shiryarwa zuwa ga aikin alheri. Aikin alheri yana shiryarwa zuwa ga Aljannah. Mutum ba zai gushe ba yana gaskiya, har sai ya zama siddiqi. Haqiqa qarya tana shiryar wa zuwa ga fajirci, shi kuma fajirci yana shiryarwa zuwa ga wuta. Mutum ba zai gushe ba yana qarya har sai a rubuta a wurin Allah maqaryaci” (Bukhari ne ya rawaito shi)
Kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce : “Alamomin munafiki guda uku ne : idan ya yi zance ya yi qarya, idan ya yi alqawari ya sava, idan aka amince masa ya yi ha’inci” (Bukhari ne ya rawaito shi)
3-Nasiha da rashin Algush
Kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Babu wani bawa da Allah zai ba shi kiwo, sannan ya mutu yana mai yi musu algush face sai Allah ya haramta masa Aljannah” (Muslim ne ya rawaito shi)
Manzon Allah (S.A.W) ya wuce da wajen wani bahon abinci, sai ya sanya hannunsa a ciki, sai ya ji lema, sai ya ce, : “Kai mai wannan abincin me ye haka?” Sai ya ce, “Ruwan sama ne ya same shi” Sai Manzon Allah ya ce, “Ina ma ka sanya shi saman abincin, don mutane su gani. Duk wanda ya yi Algush baya tare da ni”. (Muslim ne ya rawaito shi)