Allah mai qaunar bayinsa ne, yana son su, yana kusanto su, yana yi musu abin da za su yarda, kuma ya yarda da su. “Yana son su, suna son sa” (Alma’idah : 54)
“Abin qauna” .. wanda yake son Annabawansa, da mabiyansu, kuma su ma suna son shi, sun fi son shi fiye da komai, zuciyarsu ta cika da son shi, harsunansu suna cike da yabonsa, zukatansu sun tafi wajensa da so da qauna da komawa zuwa gare shi cikin dukkan al’amura.Allah yana azurta su da son mutane gare su, su so su, su karvi abin da suka zo da shi.
Makusanci abin qauna, mai son alheri ga bayinsa
Bayinsa suna son shi, suna shauqin gamuwa da shi. Ya zo a cikin hadisi : “Wanda ya so gamuwa da Allah sai Allah ya so gamuwa da shi” (Bukhari ne ya rawaito shi)
Yana umartar ka da wanke zuciya, da tsarkake ta daga gaba da qiyayayya, da wanke daga dattin qulli da ruwan so da qauna, da kashe wutar hassada da qanqarar soyayya da qauna.