Wanda bai gushe ba yana yin afuwa, yana mai siffata da afuwa da gafara, kowa yana buqatar afuwarsa da gafararsa, kamar yadda kowa yake buqatar rahamarsa da karamcinsa.
Ya wanda ya yi alqawarin gafara da afuwa ga wanda ya zo da sabubbanta. Allah Maxaukakin Sarki ya ce “Ni mai yawan gafara ne ga wanda ya tuba, ya yi imani ya yi aiki na qwarai sannan ya shiriya” (Xaha : 82)
Muna roqonka, ya mai gafara ka azurta mu da tuba na gaskiya, wadda za mu bar zunubanmu da ita, mu yi nadama akan abin da muka yi na savo da wanda ba daidai ba, kuma mu qara azama da ita a wajen bauta maka. Ka gafarta mana ya mai yawan gafara.
Ya Allah kai mai afuwa ne, kana son afuwa, ka yi mana afuwa, Ya Allah ka ba mu labari kai mai gafara ne mai jin qai.. “Ka ba bayina labari cewa nine mai gafara mai jin qai” (Al-hujrat : 49)
Ka ji qanmu, ka yi mana gafara, ya mai yawan gafara.