Allah Mai karvar tuba

Allah Mai karvar tuba

Allah Mai karvar tuba

Shi ne Allah mai karvar tuba.. “Lallai Allah mai yawan karvar tuba ne mai jin qai” (Attaubah : 118)

“Mai karvar tuba”.. Wanda bai gushe ba yana karvar tuban masu tuba, yana gafarta zunuban masu zunubi, duk wanda ya tuba zuwa ga Allah tuba na gaskiya, Allah zai karvi tubansa, shi ne wanda yake sanya masu tuba su tuba, ta hanyar datar da su, da fuskantar da zukatansu zuwa gare shi, shi ne yake karvar tubansu, idan sun tuba, ya yafe musu kurakuransu.

“Mai Karvar Tuba”

Wanda ya shar’antawa bayinsa tuba, saboda falalarsa da karamcinsa, ya yi musu alqawari da abin da ya fi haka yawa, shi ne ya sanya munanan ayyukansu su zama masu kyau.

“Mai karvar tuba”

Wanda yake tabbatar da bayi akan tubansu, ya taimake su akan abin da ya xora musu na ayyuka.

“Mai karvar Tuba”

Wanda yake datar da bayinsa zuwa ga tuba, ya kwaxaitar da su, ya sanya musu sonta.

“Mai karvar tuba”

Wanda yake karvarta daga bayinsa, ya ba su lada, ya xaukaka musu darajan, ya kankare musu zunubai, Allah mai girma da buwaya

Haqiqa shi Allah mai karvar tuba ne”



Tags: