Wanda iliminsa ya kewaye komai ciki da waje, fili da voye, wajiban abubuwa da waxanda ba za su yi wu ba, da waxanda za su yi wu, da duniyar sama da qasa, da can da yanzu, da nan gaba, babu wani abu da yake voye masa.
“Lallai Allah a wurinsa ne sanin ilimin alqiyama yake, yana saukar da ruwan sama, yana sanin abin da yake cikin mahaifa, wata rai ba ta san abin da za ta yi gobe ba, haka ma wata ran ba ta san a inda za ta mutu ba, lallai Allah shi ne masani qwararre mai ba da labari” (Luqman : 34)
“Ya san abin da yake cikin sammai da qassai, ya san abin da kuke voyewa da abin da kuke bayyanawa, Allah masanin abin da yake cikin qirji ne” (Attagaabun : 4)
Shi Allah Masani ne ga dukkan komai
“Allah wanda ya halicci sammai bakwai, kuma qasa kwatankwacinsu, yana saukar da al’amura tsakaninsu, don ku sani Allah mai iko ne a kan dukkan komai, kuma ya kewaye komai da saninsa” (Axxalaq : 12)
Allah maxaukakin Sarki ya ce, “Lallai Allah ya kewaye dukkan komai da sani” (Axxalaq : 12)