Lallai Allah shi ne Mabayyani.. “Lallai Allah shi ne gaskiya mabayyani” (Annur : 25)
Ya wanda yake Mabayyani, ka bayyana mana hanyar gaskiya, ka tseratar da mu daga haxewar hanyar gaskiya da ta qarya, ya Ubangiji.
Allah mai bayyana gaskiya ne da dukkan wasu abubuwa, a lokacin duk shakka zata kau.
Lamarin kaxaitakar Allah a bayyane yake, ba shi da abokin tarayya
Ba ya vuya ga halittarsa saboda abin da ya sanya na alamomin hankali da shari’a na zahiri, waxanda suke nuna samuwarsa da kyautarsa, da kuma ikonsa.
Wanda ya bayyanawa bayinsa hanyar gaskiya, ta hanyar aiko musu da Manzon Allah (S.A.W) da littafi bayananne.. “Haqiqa wani haske da wani littafi mabayyani sun zo muku daga Allah” (Alma’idah : 15)
Allah wanda ya bayyana hanyar sa’ida ga bayinsa, ya gwama ta da yi masa xa’a da kaxaita shi a wajen bauta.