Ya wajabta wa kansa yin rahama, kuma rahamarsa ta riga fushinsa, kuma ta yalwaci dukkan komai.. “Lallai rahamar Allah tana kusa da masu kyautatawa” (Al-aaraf : 56)
Mai rahama, mai jinqai, mai alheri, mai karamci, mai kyauta, mai jinqai, mai yawan kyauta. Waxannan sunaye ma’anoninsu suna kusa da juna, kuma dukkaninsu suna nuna siffantuwar Allah da rahama, da aikin alheri, da kyauta, da karamci, kuma suna nuna yalwar rahamar Alah wadda ta haxa komai da komai, gwargwadon yadda hikimar Allah ta hukunta. Ya kevance muminai da wani kaso mai yawa a cikinta, da rabo mai girma. Alllah ya ce, “Rahamata ta yalwaci dukkan komai, zan rubutata ta akan waxanda suke da taqawa” (Al’aaraf : 156) Ni’imomi da kyautatawa dukkansu alamu ne na rahamar Allah Maxaukakin Sarki da kyautarsa da karamcinsa, da alkhairin duniya da lahira, duk wannan alamomin rahamarsasa ne.Allah ya fi jin tausayinmu fiye da iyayenmu mata. Manzon Allah (S.A.W) ya nuna wata mace mai shayar da wani jinjiri ya ce, “Kuna ganin wannan za ta iya sanya xanta cikin wuta, sai muka ce, a’a, ba za ta iya jefa shi cikin wuta ba, sai Manzon Allah ya ce, “Allah ya fi tausayin bayinsa fiye da wannan ga xanta” (Bukhari ne ya rawaito shi)
Yana tausayin dukkan bayinsa, kuma yana da wata rahama da ya kevance ta ga bayinsa muminai “Allah ya kasance danagane da muminai mai jinqai” (Al-ahzab : 43)
Yana cikin jinqan shi aiko Muhammad (S.A.W) don ya zama rahama ga talikai, mai shiryar da su, mai kiyaye musu maslaharsu ta duniya da ta addini
Ba wanda yake riqe da rahamarsa sai shi, babu wanda yake sakinta sai shi.. “Abin da Allah ya buxe na rahamarsa ga mutane babu mai riqe shi, abin da kuma ya riqe babu mai sakinsa a bayansa, shi ne mabuwayi mai hikima” (Faxir : 2)