Ya wanda yake ba da ni’ima, ya wanda yake ba da abin nema, ya wanda yake ba da kyautatawa
Ka ba ni kyautar yardarka, ka ba ni aminci, ka ba ni sa’ada da tausayi.
Ka yi mana kyautar ka qara mana, kai ne ma’abocin kyauta da karamci “Ka ba mu wata rahama daga wajenka, haqiqa kai mai yawan bayarwa ne mai yawan jinqai” (Al-imran : 8) , “Allah mai karamci ne, yana son karamci da halaye masu girma, yana qin qasqantun halaye” (Tirmizi ne ya rawaito shi)
Yana ba wanda ya so, yana hana wanda ya so.
Kyautarsa ba ta da iyaka, ba mai mayar da falalarsa, yana cewa abu : “kasance, sai ya kasance” (Albaqra : 117)
Yana ba da arziqin fili da na voye, yana baiwa da falalarsa da karamcinsa.
Daga cikin haka abin da Allah yake buxewa bayinsa daga tunani mai kyau, da amfani, da ilimi da shiriya, da dacewa, da karva addu’a, dukkan wannan yana cikin arziki na voye da Allah yake ba da yawa daga cikin mutane.
Ya bayar, ya hana, ya sauke ya xaukaka, ya sadar, ya yanke, a hannunsa alheri yake, kuma shi mai iko ne akan komai
Shi ne Allah mai yawan bayarwa da yawan kyauta