Allah ya isarwa bayinsa, ya ishe su daga barin dukkan komai.. “Ashe Allah ba mai isa ne ga bawansa ba?” (Azzumar : 36)
&"Mai isa&"..Wanda ya kewaye da sanin komai daki-daki, ya san shi ciki da bai, ya san abin da halittunsa suka voye.Allah ya isar mana kuma madallah da abin dogara.... Annabi Ibrahim ya faxi haka yayin da aka jefa shi wuta, sai ta zama sanyi da aminci gare shi. Haka ma sahabbai sun faxe ta, kamar yadda yake cikin faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Lallai mutane sun yi yi muku taron dangi…” (Al – Imran : 173)
Sai suka ce,. “Allah ya isar mana, kuma madallah da abin dogara. Sai suka juya da ni’ima daga Allah da falala, ba wata cuta da ta same su, suka bi yardar Allah” (Al-imran : 173 – 174)
Allah ne mai hisabi, wanda yake yi wa bayinsa hisabi, yana lissafa musu ayyukansu, ya saka musu bisa ayyukansu, alheri da alheri, sharri da sharri, sakamakon abin da suka aikata. “Shi ne mafi saurin masu hisabi” (Al’an’am : 62)
Mai Isarwa.. Ya isar wa bayinsa da dukkan abin da suke nema, kuma suke buqata, ya ishi wanda ya yi imani da shi, ya dogara da shi, ya nemi buqatunsa na duniya da lahira a wajensa, ya ishe shi, isa kevantacciya,Wanda ya kewaye da sanin komai daki-daki, ya san shi ciki da bai, ya san abin da halittunsa suka voye.
Ya Ubangiji ka isar mana sharrin abin da ya dame mu, ka kimsa mana shiriyarmu, ka qara mana alheri ya mai karamci.. “Allah ya isa Gwanin Hisabi” (Annisa’i : 6)