Mai xora karyayye, mai taimakon fursuna, mai wadatar da talaka, mai tayar da masu tuntuve, mai gafarta zunuban masu zunubi, mai yanta waxanda suke cikin azaba, mai tayar da zukatar masoya masu tsoronsa.
“Al-jabbar”.. ma’ana maxaukaki, mai rinjaye, mai tausayi, mai miqar da karyayyun zukata, da gajiyayye mai rauni, da wanda ya fake a wajensa.Wanda xaukakarsa ta cika, ni’amarsa ta girmama a kan dukkan komai
Wanda komai da komai suka sunkuya masa, suka sallama masa, babu wani abu da yake shagaltar da shi daga wani abu.
Ma’abocin qasaita, da sarauta, da isasshen mulki, da girma da xaukaka
Wanda dukkan masu girman kai suka sunkuya masa, masu girma suka karaya a gabansa, masu mulki da manya suka qasqanta a gabansa, masu laifi da xagawa suka zube a gabansa.