Ya wanda yake shi kaxai ne a cikin zatinsa, shi kaxai a sunayensa, shi kaxai a siffofinsa.
Muna roqonka tsarkin zuciya da so, da fata. Ya wanda yake shi kaxai wanda ake nufi da buqata.
Tilo a cikin zatinsa, da sunayensa, da siffofinsa, baya da kishiya ko makamanci, ko kishiya ko kini. “Shin ka san takwara gare shi” (Maryam : 65)
Tilo cikin alantakarsa, wanda ya cancanci bauta, babu wani wanda za a bautawa da gaskiya sai Allah, ba a juyar da ibada kaxan ko mai yawa ga wanin Allah.
Shi kaxai tilo wanda ake nufata. Ubangiji abin bauta, dukkan zukata sun yi masa shaida, idanuwa sun ratayu da shi, masanin gaibu.
Allah ya halicci bayi akan kaxaita shi, shi kaxai, ba shi da abokin tarayya, babu wanda ya fuskanci waninsa ya samu nasara, ko ya bauta wa waninsa ya samu sa’ida, ko ya yi shirka da shi ya tsira.