Kalmar “Ilahu”
Tana nufin abin bautawa, abin yiwa xa’a, wanda ya cancanta a bauta masa.. “Ku bautawa Allah kada ku haxa shi da komai a wajen bauta” (Annisa’i : 36)
Ita ce babu abin bautawa da gaskiya sai Allah
Ta haxa rukunai guda biyu manya-manya.
Na Farko : Kore bauta ta gaskiya daga wani Allah mai girma da buwaya.
Na Biyu : Tabbatar da bautar gaskiya ga Allah maxaukakin Sarki koma bayan waninsa.. “Shi ne Allah Wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi” (Al-hashar : 22)
Kalmar Shahada (La Ilaha Illal Lahu)
Ita ce tsantsar kalmar tauhidi, kuma ita ce mafi girmar farillar da Allah da ya wajabta ta akan bayinsa, matsayinta a addini kamar matsayin kai ne a jiki.