Duniyar nan gabaxayanta tana mai tabbatarwa da shaidawa da faxin akwai Allah Mai girma da buwaya. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Manzanninsu suka ce, yanzu akwai shakka a cikin samuwar Allah, wanda ya halicci sammai da qassai, yana kiranku don ya gafarta muku zunubanku ya jinkirta musu zuwa wani lokaci sananne. Sai suka ce, kufa ba kowa ba face mutane kamar mu, kuna so ne ku kange mu daga abin da iyayenmu suke bautawa, ku zo mana da wata hujja mabayyaniya” (Ibarahim : 10)
Mumini shi ne da ya yi yaqinin cewa Allah Maxaukakin Sarki shi ne Ubangiji, mai iko, ya kuma tabbatar da cewa shi ne abin bautawa shi kaxai.Ta yaya za a nemi dalili akan samuwar abin da shi ne dalilin samuwar komai Allah mai girma da buwaya.
Idan muka tsallaka zuwa ga dalilan da suke nuna samuwar Allah, za mu samu dalilai kama haka :
Asalin halitta an yi ta ne a kan imani da Allah mahalicci. Babu wanda yake barin wannan abin da aka halicce shi a kai na imani da Allah mahalicci sai wanda Allah ya rufewa zuciya da hankali. Daga cikin manya-manyan dalilai da suke nuna an halicci mutum a kan imani da samuwar Allah Maxaukakin Sarki faxin Manzon Allah (S.A.W): “Dukkan wanda ake haihuwa ana haihuwarsa akan asalin halitta (Fixirah), iyayensa ne suka mayar da shi bayahude ko banasare ko bamajuse, kamar irin yadda dabba take haihuwa, shin kuna ganin ana haihuwar mai yankakken kunne”(Bukhari ne ya rawaito shi)
Dukkan wani abin halitta ya yarda da kaxaita Allah a yanayin halittarsa. Allah ya ce, “Ka tsayar da fuskarka a kan addini, kana mai karkata ga barin qarya. Halittar Allah ce da ya halicci mutane a kanta, babu canji ga halittar Allah. Wannan shi ne addini miqaqqe sai dai da yawan mutane ba su sani ba” (Arrum : 30)
Waxannan dalilai na hankali suna nuna samuwar Allah maxaukakin Sarki.
Tabbatuwar da samuwar Allah a hankalce ya fi kowane dalili qarfi ga duk wani wanda shaixanu ba su janye shi ba, don haka Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Halittar Allah ta asali da ya halicci mutane a kanta” (Arrum : 30)
Bayan ya ce “Ka tsayar da fuskarka ga addini kana kaucewa varna”. (Arrum : 30)
Sunan Allah suna ne da aka zana shi a cikin halittar kowa, ba ya buqatar wani dalili fiye da wannan.Lafiyayyen hankali yana shaida wa da samuwar Allah, amma wanda shaixanu suka janye shi zai iya qin wannan dalili ya ji ba ya buqatarsa. Amma idan ya faxa cikin wata matsala babba, sai ka ga hannayensa da idanuwansa da zuciyarsa sun nufi sama kai tsaya suna neman taimako da agaji daga Ubangijinsa. Domin ya koma halittarsa ta asali madaidaiciya.
Daga cikin manya-manyan dalilai masu qarfi, waxanda ba wanda zai yi musu akansu sai mai jayayyar runto kaxai, akan tabbatar da samuwar Allah mahalicci, daga cikinsu akwai :
1-Dukkan halitta akwai wanda ya halicceta : dukkan waxannan ababen halitta gabaxayansu akwai wanda ya samar da su, domin ba zai yi wu su samar da kansu da kansu ba, saboda babu abin da ya halicci kansa, don kuwa babu shi kafin samuwarsa, to kuma ta yaya zai samar da kansa, don dukkan wani abu samamme akwai wanda ya samar da shi. Sannan kuma samuwar waxannan abubuwa akan wannan tsari mai kyau, haxaxxe, mai tafiya tare da sababi, a haxe da juna, ba zai yiwu ba a ce haka kurum abun ya faru kwatsam, a’a dukkan wani mahaluki ba makawa yana da wanda ya halicce shi. To idan kuwa abin haka yake, to lallai Allah ne Ubangijin talikai ya samar da su, Allah MaxaukakinSarki ya faxi wannan dalili inda yake cewa “Shin an halicce su ne daga babu, ko kuwa su ne masu yin halittar” (Axxur : 35)
Allah yana nufin su ba haka kurum akan halicce su ba, ba tare da wani wanda ya halicce su ba, kuma ba su suka halicci kawunansu ba, to dole suna da wanda ya halicce su, wanda shi ne Allah Maxaukakin Sarki, don haka ma lokacin da Jubairu xan Mux’im – Allah ya yarda da shi – ya ji Manzon Allah (S.A.W) yana karanta suratux Xuri, ya zo kan waxannan ayoyi, inda Allah yake cewa, “Shin an halicce su ne daga babu, ko kuwa su ne masu yin halittar. Ko su ne suka halicci Sammai da Qasa, a’a ba su yi yaqini ba. Ko a wajensu akwai taskokin Ubangijinka, kai ko su ne waxanda suka mamaye komai” (Axxur : 35 – 37).
A lokacin Jubairu yana mushiriki bai musulunta ba, amma duk da haka sai ya ce, “Zuciyata ta kusa ta tsinke” (Bukhari ne ya rawaito shi)
Xan adam tare da ximbin ilimin sanin duniya da Allah ya ba shi, har yanzu ya kasa gano wasu abubuwa na voye waxanda babu abin zai kawo qarshen cece-kuce a kansu sai kawai imani da akwai Allah shi kaxai.2-Bayyanannu ayoyin Allah a cikin duniya da halittarsa. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Ku duba (ku yi tunani) mene ne a cikin Sammai da Qasa” (Yunus : 101)
Saboda a cikin duba sammai da qasa zai bayyana Allah ne mai halitta, kuma ya qara tabbatar da kaxautuwar Allah da ayyukansa. An cewa wani mutumin qauye, dame ka gane Ubangijinka? Sai ya ce, “Alamar sawu tana nuna tafiya, kashin raqumi yana nuna akwai raqumin. To yanzu sama mai matakalai, da qasa mai hanyoyi, da teku mai igiyar ruwa da yawa, yanzu waxannan ba za su nuna akwai Allah mai ji mai gani ba?”.
3-Tsaruwa lamarin duniya da kyautatuwarsa, dalili ne akan wanda yake tsara shi, shi ne abin bauta shi kaxai, kuma mamallakinsa shi kaxai, Ubangiji shi kaxai, babu wani abin bauta sai shi, kamar yadda ba zai yi wu ba a samu Ubangiji biyu, masu halitta kuma waxanda suka yi daidai da juna, to haka ma ba zai yiwu a samu ababen bauta guda biyu ba, waxanda suka yi daidai da juna. Kuma ba zai yi wu a samu waxanda suka yi duniya su biyu ba, abu ne tabbatacce a hankali, to haka ma ba za a samu abbaben bautawa guda biyu ba.
Dukkan Shari’u suna nuana samuwar wanda ya yi halitta, kuma suna nuna cikar iliminsa da hikimarsa da jinqansa, saboda dukkan shari’u ba makawa da wanda ya shar’anta su, wanda shi ne Allah Mai girma da buwaya, Allah ya ce, “Ya ku mutane ku bautawa Ubangijinku wanda ya halicce ku, da waxanda suke gabaninku ko kwa samu taqawa. Wanda ya sanya muku qasa ta zama shimfixa gareku, ya sanya kuma sama ta zama gini gareku, ya saukar daruwa daga girgije, ya fitar da ‘ya’yan itace arziqi gareku, to kada ku sanya wa Allah abokan tarayya alhali kuna sane” (Albaqra : 21 – 22)
Dukkan littattafan da Allah ya saukar suna faxin haka.
Daga bayanannun dalilai da suke nuna samuwar Allah Mahalicci akwai dalilin da duk mai hankali yake gani kuma yake jinsa, kamar :
1-Amsa addu’o’i : Mutum yana roqon Allah, ya ce, “Ya Ubangiji” ya roqi wani abu, sai kuma ya ga an amsa masa, to wannan dalili ne da ake gani dake nuna samuwar Allah Ubangiji, saboda Allah ya amsa masa, kuma mutum ya ga hakan quru-quru. Haka ma muma sau da yawa mun ji misalai a da, da yanzu na cewa Allah ya amsa musu abin da suka roqa. To wannan wani lamari ne da yake nuna samuwar Allah Mahalicci, a cikin Alqur’ani akwai dalilai irin waxannan da yawa, daga cikinsu akwai faxin Allah, “Ka tuna (Annabi) Ayyuba lokacin da ya kira Ubangijinsa cewa cuta ta shafe ni, Allah kuma kai ne mafi jinqai masu jinqai. Sai muka amsa masa” (Al’anbiya : 83 – 84)
Da ayoyi da yawa irin waxannan.
Kore samuwar Allah cuta ce a cikin hankali, kuma matsala ce a cikin tunani.2-Shiryar da halittu zuwa ga abin da yake shi ne sirrin rayuwarta. Wan ne ya shiryar da mutum zuwa ga kama mama yayi da aka haife shi? Wanene ya shiryar da Al-Hudu-Hudu har yake gane wurin ruwa a qarqashin qasa, wanda ba wanda yake ganin hakan sai shi? Haqiqa Wannan aikin Allah ne, yana cewa : “Ubangijinmu wanda ya halicci dukkan komai kuma ya shiryar da shi” (Xaha : 50)
3-Ayoyin da Allah ya aiko Annabawa da Manzanni da su, su ne Mu’ujizozin da Allah ya qarfafa su da su, ya zave su, daga cikin mutane ya fifita su. Dukkan wani Annabi Allah ya aiko shi da wata mu’ujiza zuwa ga mutanensa, tana tabbatar da cewa abin da aka aiko shi da shi daga wajen Allah ne, mahalicci abin bauta shi kaxai, babu wani abin bauta wanda ba shi ba.