1-Fita daga ruxu da shakka : To ta yaya ma wanda ya san yana da Ubangiji, wanda shi ne Ubangjijin komai zai ruxe ya shiga shakka, alhali ya san Allah shi ne ya halicce shi, ya daidaita shi, ya girmama shi ya fifita shi, ya hore masa abin da yake cikin sammai da qasa gabaxaya, ya kwararo masa ni’imominsa na zahiri da baxini, don haka sai ya nutsu da Ubangijinsa, ya koma wajensa, ya gane cewa wannan rayuwar gajera ce, tana haxe da alheri da sharri, da adalci da zalunci, da jin daxi da wahala.
Kore samuwar Allah cuta ce a cikin hankali, kuma matsala ce a cikin tunani, kuma duhu ne a cikin zuciya da tozarta a rayuwa.Amma waxanda suka yi jayayya da ayyukan Allah, suka yi shakkar gamuwa da shi, to rayuwarsu ba ta da wani xanxano ko ma’ana, dukkanta tashin hankali ne da ruxewa, da tambayoyi da dama, ba su da wani wuri da za su koma gare shi, hankalinsu ya kwanta. Koyaushe suna cikin damuwa da rashin kwanciyar hankali da ruxu da shakka. Wannan kuwa azaba ce ta duniya, wuta ce da take dukan fuskarsu safe da yamma.
2-Samun kwanciyar hankali : Hanya xaya ce ta samun kwanciyar hankali ita ce imani da Allah da ranar lahira. Imani mai qarfi na gaskiya wanda babu wata shakka a cikinsa. Wannan shi ne abin da tarihi ya nuna, kuma kowane mutum mai adalci zai tabbatar da hakan, saboda mun riga mun sani cewa mafi yawancin mutanen da suke cikin damuwa da tozarta da damuwa da shakka su ne waxanda Allah bai ba su imani da shi ba, ba su da yaqini na imani, don haka rayuwarsu ba ta da wani xanxano ko zaqi, koda kuwa an lulluve su da kayan daxi, saboda rayuwarsu ba ta da wata ma’ana, ba su gane sirrinta ba, to ta yaya zasu samu nutsuwa a cikin zukatansu da kwanciyar hankali.
Imani shi ne kwala-kwalen tsiraSamun nutsuwa wata fa’ida ce daga fa’idojin imani da Allah, saboda kaxaita Allah (Tauhidi) wata bishiya ce mai tsarki, wadda take ba da ‘ya’yanta a kowane lokacin da izinin Ubangijinta, wata kyauta ce daga sama Allah yake saukar da ita akan zukatan muminai, don su samu tabbata yayin da mutane suka raurawa, su yarda yayin da mutane suka yi fushi, su yi yaqini yayin da mutane suke shakka, su yi haquri yayin da mutane suka haukace, wannan nutsuwar ita ce wadda Allah ya raya zuciyar Manzon Allah (S.A.W) da ita a ranar hijira, don haka babu wani tsoro ko baqin ciki ko wata damuwa da ta same shi. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “In ma ba ku taimake shi ba, to Allah ya taimake shi yayin da kafirai suka fitar da shi, suna su biyu a cikin kogo, a lokacin da ya cewa abokinsa, kada ka damu, Allah yana tare da mu”. (Attaubah : 40)
Duk wanda ya wadatu da Allah, sai mutane su buqace shi.Damuwa da tsoro ya riga ya kama zuciyar abokinsa Abubakar Assidiq, ba wai tsoron rayuwarsa ba, a’a yana tsoron abin da zai sami Manzon Allah (S.A.W) da kiran da ya zo da shi na kaxaita Allah, har Sayyidina Abubakar lokacin da ya ga maqiya sun kewaye kogon da suke ciki sai ya ce : “Ya Manzon Allah da xayansu zai duba qasan dugadagansa da ya ganmu, sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce masa, yana mai kwantar masa da hankali, “Ya Abubakar mene ne zatonka da mutane biyun da Allah ne na ukunsu”. (Muslim ne ya rawaito shi)
Duk lokacin da alakarka da Allah ta yi rauni to shakka da waswasi za su yi ta bijiro maka cikin zuciya.Wannan nutsuwa wata rayuwa ce daga Allah, kuma haske ne da mai tsoro yake nutsuwa a cikinsa, wanda yake cikin tashin hankali ya samu nutsuwa, wanda yake cikin damuwa ya samu rarrashi a cikinta, mai rauni ya samu qarfi, rikitacce ya samu shiriya. Wannan nutsuwar qofa ce da Allah yake buxewa muminai daga cikin bayinsa, daga nan suke samun iskarta mai daxi, haskenta yake haskaka musu, suke samun qanshin turarenta, saboda Allah ya xanxana musu sakamakon abin da suka aikata na alheri, kuma ya nuna musu xan qaramin misalin abin da yake jiransu, sai su sami ni’ima da aminci da rayuwa da daga wannan iskar wannan nutsuwar.
3-Samun Yarda da aminta da Allah : komai yana hannun Allah, har amfani da cuta, Allah Maxaukakin Sarki shi ne mahalicci, shi ne mai azurtawa, mamallakin komai, mai jujjuya al’amura, dukkan makullan sammai da qasa suna hannunsa, don haka yayin da mumini ya san cewa babu wani abin da zai same shi sai abin da Allah ya rubuta msa, na alheri ko sharri, na amfani ko cutuwa, koda kuwa dukkan halitta sun haxu akan yi masa savanin abin da Allah Ya qaddara masa, to ba hakan ba zai tasiri ba a kanshi har abada, saboda ya san Allah shi ne mai amfanarwa da cutarwa, shi kaxai ne mai bayarwa da hanawa, sai sanin hakan ya qara wa mumini aminci da yarda da Allah mai girma da buwaya, da kaxaita Allah, don haka ma Allah ya zargi wanda yake bautawa abin da baya amfanarwa baya cutarwa, baya wadatawa wanda yake bauta masa da komai, Allah yana cewa, “Dukkan makullan Sammai da qasa na Allah ne. waxanda suka kafirce wa ayoyin Allah waxannan sune hasararru”. (Azzumar : 63)
Zuciya a hargitse take babu wani abin da zai haxa ta wuri guda, sai fuskantar Allah. A cikinta akwai kewa babu abin da zai gusar da ita sai kaxaita Allah da xebe kewa da shi. A cikinta akwai damuwa da baqin ciki babu abin da zai tafiyar da su sai farin cikin sanin Allah da mu’amalar gaskiya tare da shi.4-Gimama Allah : Tasirin girmama Allah a fili yake a rayuwar mumini, wanda ya yi imani da Allah, ya kaxaita shi da bauta, da nufi da yin abu don shi, a duk lokacin da mumini ya lura da abin da Allah yake da shi na mulkin sammai da qasa to babu abin da zai yi face ya ce, “Ilimin Ubangijina ya yalwaci komai” (Al’an’am : 80)
Yana cewa, “Ya Ubangijina ba ka halicci wannan don wasa ba, tsarki ya tabbata a gareka” (Al-Imran : 191).
Duk wannan yana nuna ratayuwar zuciya da Ubangiji mahallicci mai girma da buwaya, da ba da qoqari wajen neman yardarsa, da qoqari wajen girmama shari’arsa da al’amuransa, da rashin yin shirka da shi, da haxa shi da wanda ba ya mallakar kansa, ba ya iya mallakawa waninsa daidai da qwayar zarra a cikin qasa da sama, dukkan wannan girmama Allah ne, kuma kaxan ne daga cikin tasirin kaxaita Allah ne a cikin ayyukansa ga mumini.