Imani Da Haxuwa Da Allah

Imani Da Haxuwa Da Allah

Imani Da Haxuwa Da Allah

Dukkan halittu za su koma zuwa ga Allah, gare shi makomarsu, kuma wannan rukuni ne tabbatacce daga rukunin imani da Allah, kai! Yana ma cikin rukunan imani. Yana daga cikin rukunan imani, imani da ranar lahira, ya tabbata lokacin da Mala’ika Jibril ya tambayi Annabinmu (S.A.W) a gaban sahabbansa yana mai koyar da su – dangane da rukunan imani sai ya ce, “Ka yi imani da Allah, da Mala’ikunsa, da littattafansa, da Manzanninsa, da ranar lahira, ka yi imani da qaddara, alherinta da sharrinta” (Muslim ne ya rawaito shi)

An kirata da ranar qarshe, saboda ba wata rana a bayanta, inda ‘yan Aljannah za su tabbata a gidajensu, ‘yan wuta ma a gidajensu. Ranar qarshe ta zo da sunaye da yawa a cikin Alqur’ni mai girma, wanda hakan yana nuna girman ranar da matsayinta da abin zai faru a cikinta, daga cikin sunayen rana qarshe akwai : Mai aukuwa (Alwaqi’a) saboda tabbacin faruwarta, akwai mai xagawa da saukewa (Khafidatun Rafi’ah) saboda za ta xaukaka wasu mutane a Aljannah, ta kuma sauke wasu a cikin wuta. An kirata da ranar hisabi da sakamako (Yaumul Hisabi wal Jaza’i waddini), an kirata ranar tabbatarwa (Yaumul Haaqqa) a ranar labarun da Allah ya bayar suke tabbata. Daga cikin sunayenta akwai (Axxaamma) ma’ana mai rinjaye, akwai kuma (Assakkha) mai qara saboda qararta tana sa kurumta, haka ana kiranta (Yaumul Wa’id) ranar narkon azaba, saboda alqawarin azaba da Allah ya yi zai tabbata. Ana kiranta da (Yaumul Hasarat Wannadamah) saboda abin zai kasance a cikin na hasara da nadama, (Yaumut Talaqi) ranar haxuwa, saboda kowa da kowa za a haxu a wuri xaya, (Yaumul Azifa) rana ta kusa, saboda kusancinta. (Yaumut Tanadi) ranar kiraye – kiaraye, saboda kiraye-kirayen da za a yi a cikinta, Yan Aljannah su kira ‘yan wuta, ‘yan wuta su kira yan Aljannah. (Yaumul Aqeem) wato bakararrar rana, saboda babu wata rana a bayanta ko a gabanta. Hakanan ana kiranta (Addarul Akhirah) gidan qarshe, da (Darul Qarar) gidan tabbata, da (Algashiya) mai lulluvewa, saboda tana lulluve mutane, da sauran irin waxannan sunaye nata

Abin da Imani da ranar Lahira ya qunsa :

Na Farko : Imani Da Abin da Yake Bayan Mutuwa

Na daga fitinar qabari:

Ita ce tambayar mamaci dangane da Ubangijinsa da addininsa da Annabinsa bayan an binne shi, sai Allah ya tabbatar da waxanda suka yi imani da magana tabbatacciya, sai ya ce, “Ubangijina Allah, addinina musulunci, Annabina Muhammad” Kuma Allah ya vatar da azzalumai, sai kafiri ya ce, “Haa haa!! Ban sani ba” sai munafiki ko mai shakkah ya ce, “Ban sani ba, na ji mutane suna faxar abu ne nima na faxa”.

Da azabar qabari da ni’imarsa:

Ita dai azabar qabari tana kasancewa ga Azzalumai da Munafikai da Kafirai, da wasu daga cikin Muminai masu savo. Allah ya ce, “Da za ka ga Azzalumai yayin da suke cikin mayen mutuwa, Mala’iku sun shimfixa hannayensu (suna cewa) ku fito da rayukanku, a yau za a saka muku da azabar wulaqanci saboda munanan abin da kuka kasance kuna faxa a kan Allah, wanda bana gaskiya ba, da kuma abin da kuka kasance kuna yin isgili da ayoyin (Allah) (Al-an’am : 93)

Sayyidina Usman ya kasance yana kuka, idan ya tsaya a kan qabari. har ya jiqa gemunsa, sai aka ce da shi, “Kana tuna Aljannah da Wuta amma baka kuka, amma kana kuka don wannan? Sai ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Qabari shi ne farkon gida daga gidajen lahira, idan mutum ya tsira daga gare shi, to abin da zai zo bayansa ya fi shi sauqi, in kuwa bai tsira daga gare shi ba, to abin da zai zo bayansa ya fi shi tsanani” sai ya ce, “Ban tava ganin wani abu mai ban tsoro ba, face qabari ya fi shi ban tsoro” (Ahmad ya rawaito shi)

Kuma Allah ya ce a kan mabiya Fir’auna : “Wuta ce ake bijirar da su a kanta safe da yamma, a ranar da Alqiyama za ta tashi, za a ce ku shigar da mabiya Fir’auna matsananciyar azaba” (Gafir : 46)

A cikin hadisin Zaid xan Sabit, daga Annabi (S.A.W) ya ce, “Ba don kada ku qi binne mamata ba, da na roqi Allah ya jiyar daku wani abu daga azabar qabari, irin abin da nake ji” Sannan sai Annabi (S.A.W) ya juyo da fuskarsa wajenmu, ya ce, “Ku nemi tsarin Allah daga azabar qabari” Sai muka ce, “Muna neman tsarin Allah daga azabar qabari” Sai ya sake cewa, “Ku nemi tsari daga azabar qabari” sai muka ce, “Muna neman tsarin Allah daga azabar qabari” sai ya ce, “Ku nemi tsarin Allah daga fitina ta voye da ta sarari”sai muka ce, “Muna neman tsarin Allah daga fitina ta fili da ta voye” Sai ya ce, “Ku nemi tsarin Allah daga fitinar Dujal” (Muslim ne ya rawaito shi)

Amma ni’imar qabari kuwa tana kasancewa ne ga muminai masu gaskiya, Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Haqiqa waxanda suka ce Ubangijinmu Allah, sannan suka daidaita, to Mala’iku suna sauka a gare su, suna cewa kada ku ji tsoro kada ku yi baqin ciki, ana muku bushara da Aljannah, wadda aka kasance ana muku alqawarinta” (Fussilat : 30)

Kuma Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Ina ma lokacin da rai ya kai maqogwaro. A lokacin ku, kuna kallo. Mu kuma mun fi kusa da shi fiye da ku, amma ba kwa gani. Ina ma kun kasance ba waxanda ake yiwa hisabi ba. Zaku dawo da ran in kuna da gaskiya. To amma idan ya kasance daga waxanda suke makusanta. To hutu da aljannar ni’ima da arzikin abinci sun tabbata gare shi. To amma idan ya kasance daga ma’abota dama. Sai a ce masa aminci ya tabbata gareka daga ma’abota dama. Kuma amma in idan ya kasance daga masu karyatawa vatattu. To yana da wata liyafa ta ruwan zafi, da qonuwa da wutar Jahim. Lalle wannan tabbas ita ce gaskiya ta yaqini. Saboda haka ka tsarkake sunan Ubangijinka Mai girma. (Alwaqi’a : 83 – 96)

Manzon Allah (S.A.W) ya ce idan mumini ya amsa wa Mala’iku biyu masu tambaya a qabari sai a ce, “Mai kira daga sama zai yi kira, ya ce, bawana ya yi gaskiya, ku shimfixa masa shimafixa na Aljannah, ku sanya masa tufafi daga Aljannah, ku buxe masa qofa zuwa Aljannah. Sai qanshinta da iskarta su shigo masa, a faxaxa masa qabarinsa iya ganinsa” (Ahmad ne ya rawaito shi a cikin wani hadisi dogo)

Na biyu : Imani Da Tashi Bayan Mutuwa

Shi ne raya matattu yayin da aka yi busa qaho karo na biyu, sai mutane su tsaya ga Ubangijin talikai, marasa takalma, tsirara basu da tufafi, da lova a tare da su. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Kamar yadda muka farar da halitta za mu mayar da ita, alqawari ne na gaskiya akanmu, haqiqa mu masu aikatawa” (Al’anbiya : 104)

Tashi bayan mutuwa abu ne tabbatacce na gaskiya, Alqur’ani da Sunnah da Ijma’in musulmi sun nuna haka, Allah ya ce, “Sannan haqiqa ku bayan haka matattu ne. Sannan ku za tashe ku ranar Alqiyama” (Almuminuna : 15 – 16)

Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Za a tara mutane ranar Alqiyama, babu takalma, babu kaciya” (Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi).

Kuma musulmai sun haxu akan tabbatuwar wannan abu, kuma wannan ce hikimar da Allah ya sanya wa bayi makoma, wadda zai saka musu a cikinta, akan abin da ya xora musu ta harshen Manzanninsa. Allah maxaukakin Sarki ya ce, “Yanzu kuna zaton mun halicce ku ne don wasa, kuma ku baza ku dawo wajenmu ba” (Almumina : 115).

Allah Maxaukakin Sarki ya cewa Annabinsa (S.A.W) “Haqiqa wanda ya saukar maka da Alqur’ani zai dawo da kai zuwa ga makoma” (Alqasas : 85)

Abu Na Uku : Imani Da Abin Da Ya Zo Na Alamomin Tashin Alqiyama

Su ne alamomin da suke fara zuwa kafin tashin Alqiyama, suna nuna ta kusa zuwa, an raba su gida biya, qanana da manya.

Qananan Alamomi:

Su ne alamomin da yawanci sukan zo tun gabanin Alqiyama da lokaci mai tsawo, akwai waxanda sun zo sun wuce, sun qare, akwai waxanda suke maimaituwa, akwai waxanda sun faru, kuma suna ci gaba da faruwa, akwai waxanda kuma har yanzu ba su faru ba, amma za su faru kamar yadda Manzon Allah (S.A.W) mai gaskiya abin gaskatawa ya faxa, misalin irin waxannan qananan alamomin akwai, aiko Annabi (S.A.W) da mutuwarsa, da buxe Baitil Maqdis, da bayyanar fitintinu, da rashin amana, da xauke ilimi da bayyanar jahilci, da yaxuwar zina da riba, da bayyanar kayan kixe-kixe, da yawan shan giya, da dogayen gine-gine da makiyaya za su yi, da yawan savawa iyaye daga ‘ya’yansu, har su riqa yi wa iyayen mu’amala kai ka ce su ne iyayen gidansu, da yawan kashe-kashe, da yawan girgizar qasa, da bayyanar kisfewa da shafewa, da bayyana ‘yan mata masu sanya tufafin tsiraici kuma suna tsirara, da yawan shaidar zur, da voye shaidar gaskiya, da sauransu da yawa waxanda suka zo a Alqur;ani da hadisin Manzon Allah (S.A.W).

Manyan Alamomi:

Wasu al’amura ne manya-manya waxanda bayyanarsu tana nuna kusancin tashin alqiyama, saura qiris ta tashi, alamomin guda goma ne, su ne, Dujal, saukar Annabi Isa xan Maryam, Yajuju da Majuju, kisfewa guda uku, xaya a gabas, xaya a yamma, xaya a tsibirin larabawa, sai ganin wani hayaqi, sai vullowar rana daga mafaxarta, sai fitowar Dabba, sai wuta wadda za ta kora mutane zuwa ga matattararsu. Waxannan alamomi za su fito xaya bayan xaya, duk wadda ta fara bayyana to sauran na biye da ita.

Abu Huxu : Imani Da Abin Da Zai Zo Na Ban Tsoro Ranar Alqiyama, kamar

1-Rugurguza manya-manyan duwatsu, da maida su qasa, da daidaita su da qasa. Allah ya ce, “Zaka ga duwatsu kana zatonsu a kafe suke, sai ka ga suna wucewa kamar yadda girgije yake wucewa” (Annamli : 88)

Ya ce, Kuma aka nike duwarwatsu nikewa, suka zamo kura abar daidaitawa (Alwaqi&"a : 5 – 6)

Ya ce, “Duwatsu za su zama kamar audugar da aka kaxa” (Alma’arij : 9)

Allah ya ce, “Suna tambayarka akan duwatsu, ka ce, Ubangijina zai sheqe su sheqewa. Ya bar su faqo fetal. Ba za ka ga wani kwari ko tudu ba a cikinsu” (Xaha : 105 -107)

2-Fashewar koguna, saboda za su kama da wuta, waxannan koguna da suka xau kaso mai yawa a bayan qasa zasu fashe a wannan rana, Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Idan koguna suka fashe” (Al-infixar : 3). “Idan tekuna aka qone (ruwan) su” (Attakwir : 6)

3-Za a canza wannan qasar da mutane suka saba da ita, haka ma sammai, sai a tashi mutane a kan wata qasa daban wadda ba su komai nata ba. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Ranar da za a canza qasa ba wannan qasar ba, haka ma sammai, sun fito zuwa ga Allah Shi kaxai mai rinjaye” (Ibrahim : 48).

Ya ce, “Za a tara mutane ranar Alqiyama a wata farar qasa mai jaja-jaja, kamar gurasar farin gari. Babu wata alama ta wani a kanta” (Bukhari da Muslim ne ya rawaito shi)

Sai ta wayi gari fili fetal babu wata alama

4-Mutane za su ga abin da basu saba da shi ba, don za su ga wata da rana sun haxu, sai tsoro ya qaru a zukata. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Yayin da gani ya ximauce. Kuma hasken wata ya dusashe. Kuma aka tara rana da wata (a wuri guda) (Alqiyama : 107)

5-Busa a cikin qaho, wanda shi ne qarshen wannan rayuwar ta duniya, idan ranar ta zo za a yi busa a cikin qaho, sai wannan busa ta kawo qarshen duk wata rayuwa a sama da qasa. “Aka yi busa a cikin qaho, sai duk wanda yake cikin sammai da qassai su sume sai wanda Allah ya so” (Azzumar : 68)

Busa ce mai ban tsoro, mai rushe komai da komai, mutum yana jin ta, ba zai iya wasiyya da komai ba, kuma ba zai iya komawa wajen iyalansa da abokanansa ba. “Ba komai suke jira ba sai busa xaya, wadda za ta kama su, sai ga su suna husuma. Ba za su iya wata wasiyya ba, kuma ba za iya komawa iyalansu ba” (Yaasin : 49 – 50)

Kuma ya ce “Sannan aka yi busa a qaho, babu wanda zai ji wannan busar face sai ya xaga wuyansa, ko gefen wuyansa, Farkon wanda zai ji wannan busa wani mutum ne da yake gyara wurin shan ruwan raquminsa, sai ya sume. Dukkan mutane su ma sumanci” (Muslim ne ya rawaito shi)

6-Taruwar da ta haxa dukkan halittun da Allah ya halitta har zuwa na qarshensu a filin taruwa. Za su taru a kan qasar mattattara tun daga farkonsu har zuwa na qarshensu, aljanunsu da mutanensu, kai har ma dabbobinsu. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Haqiqa a cikin haka akwai aya ga duk wanda yake tsoron azabar lahira, wannan rana ce da za a tara mutane a cikinsa, kuma yini ne wanda ake halarta” (Hud : 103).

Allah Maxaukakin Sarki ya ce “Ka ce, Haqiqa na farko da na qarshe za a tara su zuwa wani lokaci a wani yini sananne” (Alwaqi’a : 49 – 50).

7-Za a tara mutane tsirara kamar yadda Allah ya halicce su, ba kuma wanda zai kalli wannan saboda tsananin wannan tsayuwa mai ban tsoro. Nana Aishatu Uwar Muminai – Allah ya yarda da ita – ta yi mamakin hakan, An karvo daga gareta ta ce, Manzon Allah ya ce, “Za a taraku marasa takalma masu lova” Sai Aisha ta ce, “na ce ya Manzon Allah, maza da mata, shashinsu yana kallon sashi? Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Ai tsananin lamarin ya fi haka, balle su damu da haka”. (Bukhari ne ya rawaito shi)

8-Ramawa wanda aka zalunta daga wanda ya zalunce shi, har dabbobi, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Wallahi za ku mayar da haqqoqi ga masu su ranar alqiyama, har dabba marar qaho sai an karvo mata haqqinta daga dabba mai qaho” (Muslim ne ya rawaito shi)

Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Duk wanda ya zalunci xan uwansa, a mutuncinsa ko wani abu na shi, to su warware tun daga nan duniya, tun kafin ranar da babu dinari ko dirhami, idan yana da kyakkyawan aiki sai a xiba daga wajensa gwargwadon zaluncin da ya yi, idan kuma baya da kyawawan ayyuka, to sai a xebo munanan ayyukan abokin a xora masa” (Bukhari ne ya rawaito shi)

9-Kusantowar rana zuwa ga mutane, har su nutse cikin guminsa, gwargwadon ayyukansu. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Za a kusanto da rana a ranar alqiyama ga halitta, har ta zama a kansu daidai da mil xaya. Sulaim xan Amir ya ce, “Wallahi ban sani ba, me yake nufi da mil, yana nufin mil na nisan tafiya, ko kuma yana nufin mishin da ake sa kwalli da shi. Manzon Allah ya ci gaba da cewa, “Sai mutane su zama a cikin gumi gwargwadon ayyukansu, daga cikinsu akwai wanda gumi zai kawo masa zuwa idon qafa, daga cikinsu akwai wasu zuwa gwiwa, daga cikinsu akwai wanda zuwa wuyansa, akwai wanda gumi zai masa linzami. Ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya yi nuni da hannunsa zuwa bakinsa” (Muslim ne ya rawaito shi)

10-Akwai wanda zai karvi littafinsa da hannun damansa, akwai wanda zai karva da hagunsa. Sai mutane su zauna a cikin ruxani da rikicewa, har kowacce takardar aiki ta faxa hannun mai ita, sai muminai su yi murnar kusantowar tsira, a yayin da suka ga takardunsu a hannuwansu na dama, a lokacin kafirai da munafukai zasu qara samun baqin ciki da damuwa yayin da suka ga takardunsu a hannayensu na hagu. Kuma wannan sakamako ne wanda ya dace. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Amma wanda aka ba littafinsa a hannun damarsa, sai ya ce, ku zo ku karanta littafina. Haqiqa ni na tabbatar zan gamu da sakamakona. Yana cikin rayuwa yardaddiya. A cikin Aljannah maxaukakiya. Ababen tsinkarta dab-dab-dab suke. (za a ce) ku ci ku sha hankali kwance, saboda abin da kuka gabatar a kwanakin da suka wuce. Amma wanda aka bawa littafinsa da hannun hagunsa, sai ya ce, kaicona ina ma ba a ba ni littafina ba. Ban san menene sakamakona ba. Kaicona wannan mai halakarwa ce. Dukiyata bata wadata min komai ba. Hujjata da mulkina sun vace min” (Alhaqqa : 19 – 29).

11-Abin da zai samu mutane na tsoro da razana, har ya zamana mutum ba zai tambayi kowa ba, ba wanda zai dame shi sai kansa. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Ranar da dukiya da ‘ya’ya ba sa amfani” (Ashu’ara : 88)

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Ranar da mutum yake gujewa xan uwansa. Da babarsa da babansa. Da matarsa da ‘ya’yansa. Kowanne mutum a cikinsu a wannan ranar yana da sha’anin da ya ishe shi” (Abasa : 34)

Abu Na Biyar : Imani Da Hisabi Da Sakamako :

Za a yiwa kowanne bawa hisabi akan aikinsa, a saka masa akan abin da ya aikata. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Makomarsu tana garemu. Sannan hisabinsu yana wajenmu” (Algashiya : 25 – 26)

Kuma Ya ce, “Duk wanda ya zo da kyakkyawa to yana da goma irinta. Wanda ya zo da mummuna to za a saka masa sai dai irinta, kuma baza a zalunce su ba” (Al’an’am : 160).

Kuma Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Mun sanya ma’auni na gaskiya saboda ranar alqiyama, ba za a zalunci wata rai da komai ba, Idan kuwa akwai wani abu daidai da qwayar zarra zamu zo da shi, mun isa masu yin hisabi” (Al’anbiya’a : 47).

An karvo daga Abdullahi xan Umar – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Haqiqa Allah zai kusanto kusa da mumini, sai ya sanya masa sitirarsa, ya rufe shi, sai ya ce, kasan zunubi kaza, kasan zunubi kaza? Sai ya ce, eh ya Ubangiji. Har sai ya yarda da laifukansa, ya tabbatar ya halaka, sai Allah ya ce, “Na sitirtaka a duniya, a yau ma zan gafarta maka” Sai Manzon Allah ya ce, “Sai a ba shi littafin kyawawan ayyukansa. Amma kafirai da Munafikai sai a yi musu shela a gaban halittu, a ce, “Waxannan su ne waxanda suka yi wa Ubangijinsu qarya. Ku saurara tsinuwar Allah ta tabbata akan Azzalumai”(Hud : 18) (Bukhari da Muslim ne ya rawaito shi).

Ya kuma inganta daga Annabi (S.A.W) cikin abin da ya rawaito shi daga Ubangijinsa mai girma da buwaya, ya ce, “Haqiqa Allah ya rubuta abubuwa masu kyau da munana, sannan ya bayyana haka, duk wanda ya yi niyyar kyakkyawan aiki, amma bai yi ba, to Allah zai rubuta masa ladan kyakkyawa guda xaya cikakkiya. Idan kuwa ya yi niyya kuma ya aikata, to Allah zai rubuta masa kyakkyawa goma, zuwa ninkin xari bakwai, zuwa ninki da yawa. Idan ya yi niyyar mummuna, amma bai aikata ba, sai Allah ya rubuta masa kyakkyawa guda xaya cikakkiya, in kuwa ya yi niyya kuma ya aikata, to sai Allah ya rubuta masa mummuna xaya” (Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi).

An cewa Hasanul Basariy : Mun ga Tabi’ai sun fi Sahabbai yawan ibada, to dame sahabbai suka fi su? Sai Alhassan ya ce, “Waxannan suna bauta amma duniya tana cikin zukatansu, sahabbai kuwa suna bauta amma lahira ce a zuciyarsu”.

Musulmai sun haxu (Ijma’i) akan tabbatar da hisabi da ba da sakamakon ayyuka, kuma wannan ce hikimar da ta sa Allah ya saukar da littattafai, ya aiko manzanni, ya wajabtawa bayi yin imani da shi, ya yi alqawarin azaba ga wanda bai bi shi ba, kuma bai yi imani da shi ba, bai bi manzanninsa ba, ya yi masa alqawarin azaba mai tsanani da azaba mai raxaxi. Da a ce babu wani hisabi, babu wani sakamako, da abin ya zama wasa, wanda Allah ya tsarkaka ga barinsa. Allah ya yi nuni da haka, inda ya ce, “Wallahi tabbas sai mun tambayi waxanda muka aikawa manzanni, kuma wallahi sai mun tambayi Manzannin. Kuma zamu ba su labari da ilimi, bamu kasance masu fakuwa ba” (Al-aaraf : 6 – 7).

Abu Na Shida : Imani Da Aljannah Da Wuta :

Su ne makoma na har abada ga halitta. Aljannah gidan ni’ima ce, wadda Allah ya tanade ta don muminai masu tsoron Allah, waxanda suka yi imani da abin da Allah ya wajabta musu, suka tsayu da yi wa Allah da Manzonsa, suna masu tsarkake zuciyoyinsu, masu bin Annabinsa. A cikin Aljannah akwai ni’ima kala-kala, “Abin da ido bai tava gani ba, kunne bai tava ji ba, tunani bai tava tunanwa ba” Allah ya ce, “Waxanda suka yi imani kuma suka yi aiki na qwarai waxannan su ne fiyayyun halitta. sakamakonsu a wajen Ubangijinsu Aljanatai waxanda qoramu suke gudana a qarqashinsu, suna masu dauwama a ciki har abada, Allah ya yarda da su, suma sun yarda da su. Wannan (sakamako ne) ga wanda ya ji tsoron Ubangijinsa” (Albayyinah : 7 – 8).

Kuma Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Wata rai bavta san me aka voye musu ba na farin ciki, sakamakon abin da suka kasance suna aikatawa”. (Assajda : 17)

Mafi girman ni’imar aljannah ita ce ganin Allah maxaukakin Sarki Allah ya ce : “Wasu fuskokin a wannan rana masu haske ne. masu kallon Ubangijinsu” (Alqiyama : 22 – 23).

Allah Mai girma da buwaya ya ce, “Waxanda suka kyautata suna da sakamako mafi kyau da qari a kan hakan”. (Yunus : 26)

Sakamako mafi kyau : shi ne Aljannah. Qarin kuwa shi ne ganin Allah mai girma, kamar yadda Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Idan ‘yan Aljannah suka shiga Aljannah, ya ce, sai Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Kuna son in qara muku wani abu? Sai su ce, “Ashe ba ka haskaka fuskokinmu ba, ka tseratar da mu daga wuta? Ya ce : Sai ya yaye musu hijabi (su ga Allah) babu wani abu da aka ba su da suka fi so irin gani Ubangijinsu mai girma da buwaya, sannan sai Manzon Allah (S.A.W) ya karanta wannan ayar : “Waxanda suka kyautata suna da sakamako mafi kyau da qari”. (Yunus : 26) (Muslim ne ya rawaito shi)

Ita kuwa wuta gidan azaba ce, wadda Allah ya tanade ta don kafirai azzalumai, waxanda suka kafirce masa, suka savawa Manzanninsa. A cikinta akwai kala-kalar azaba da narko, wadda ba ka tava tunani ba. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Ku ji tsoron wuta wadda aka tanada don kafirai” (Ali-Imran : 131).

Kuma Ya ce, “Haqiqa mun tanadarwa da azzalumai wata wuta da gadajenta sun kewaye ta, idan suka nemi taimako sai a basu wani ruwa mai kama da tafasasshen mai, yana qona fuskoki, tir da abin sha, kuma wurin hutu ya munana. (Alkahfi : 29)

Kuma Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Tabbas Allah ya la’anci kafirai ya kuma tanadar musu da wutar sa’ira. Suna masu dauwama a cikinta har abada, baza su samu wani majivincin lamari ba ko mataimaki. A ranar da za a juya fuskokinsu a wuta, suna cewa ya kaiconmu ina ma mun bi Allah mun bi Manzo” (Al’ahzab : 64 – 66)

Mafi samun saukin azaba – Allah ya kare mu – shi ne wanda Manzon Allah (S.A.W) ya ambata, ya ce, “Mafi saukin yan wuta a azaba ranar alqiyama, shi ne mutumin da za a sanya masa garwashi a tafin qafafunsa, tana tafarfasa qwaqwalwarsa” (Bukhari ne ya rawaito shi)

Fa’idojin Imani Da Ranar Qarshe :

1-Tabbatar da rukuni daga cikin rukunan imani, saboda Imani da Allah ba ya tabbata har sai an yi imani da ranar qarshe, domin yana cikin rukunan imani, don haka ma Allah ya wajabta mana yaqar wanda bai yi imani da shi ba. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Ku yaqi waxanda ba su yi imani da Allah da ranar lahira ba” (Attaubah : 29).

2-Samun aminci duniya da lahira, da alqawarin lada mai girma. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Ku saurara, haqiqa waliyyan Allah babu tsoro a kansu, kuma ba sa baqin ciki”. (Yunus : 62).

3-Alqawarin lada mai girma, Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Haqiqa waxanda suka yi imani da waxanda suke yahudu da nasara da masu bautawa taurari duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira ya yi aiki na qwarai suna da ladansu a wajen Ubangijinsu, babu tsoro a kansu, kuma ba su baqin ciki”. (Albaqara : 62).

Uwar Muminai A’isha ta fadawa wata mata cewa, ki yawaita ambaton Allah zuciyarki za ta yi laushi.

4-Kwaxaitarwa akan ayyukan alheri. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Ya ku waxanda suka yi imani, ku bi Allah, ku bi Manzonsa, da ma’abota al’amari a cikinku. Idan kuka yi jayayya a cikin wani abu to ku mayar da shi ga Allah da Manzonsa, in kun kasance kun yi imani da Allah da ranar lahira. Wannan shi ne alheri kuma mafi kyau ga makoma”. (Annisa’i : 59).

Kuma Ya ce, “Kaxai waxanda suke raya masallatan Allah su ne waxanda suka yi imani da Allah da ranar Lahira”. (Attaubah : 18)

Kuma Ya ce, “Kuna da abin koyi kyakkyawa a wajen Manzon Allah, ga wanda yake fata ga Allah da ranar lahira, ya ambaci Allah da yawa” (Alahzab : 21)

Kuma Ya ce, “ Kuna da abin koyi kyakkyawa a wajen Manzon Allah, ga wanda yake fata ga Allah da ranar lahira” (Al-Mumtahana : 6)

Alhasan - Allah ya yarda da shi - ya ce, “Wanda duk ya san mutuwa, to masifun duniya za su yi masa sauqi”

Ya ce, “Ku yi shaida don Allah, wannan shi ne abin da ake wa wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira wa’azi da shi”. (Axxalaq : 2)

5-Yana hana aikata munanan ayyuka Ubangijinmu Allah ya ce, “Ba ya halatta gare su (mata) su voye abin da Allah ya halitta a cikin mahaifansu, in har sun yi imani da Allah da ranar lahira” (Albaqra : 228)

Kuma Ya ce, “Idan kun saki mata, suka gama iddarsu, to kada ku hana su su aure mazajensu idan sun yarda da hakan a tsakaninsu da adalci, wanna shi ne abin da ake wa wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira wa’azi da shi”. (Albaqra : 232)

Kuma Ya ce, “Waxanda suka yi imani da Allah da ranar lahira ba sa neman izininka a kan barin jihadi da dukiyoyinsu da rayukansu, Allah ya san masu tsoran shi. Waxanda ba su yi imani da Allah da ranar lahira ba, waxanda suke shakka, su ne suke naman izininka a kan barin jihadi, suna cikin shakkarsu suna kai kawo” (Attaubah : 44 – 45)

Zuciya ba ta gyaruwa, bata rabauta, ba farin ciki, ba ta jin daxi, ba daxaxa, ba ta nutsuwa, sai da bautawa Ubangijinta da komawa gare shi.

Shaikhul Islam

Don haka wanda bai yi imani da wannan rana ba, ba ya takatsantsan wajen aikata haramun, kuma ba ya jin kunyar haka. “Ba ni labarin wanda yake qaryata ranar sakamako. Mai irin wannan shi ne yake hankaxe maraya. Kuma ba ya kwaxaitarwa a bisa ciyar da miskini” (Alma’un : 1 – 3)

6-Rarrashin mumini akan abin da ya kubce masa na duniya, saboda abin da yake sa ran samu na ladan lahira da sakamakonta. Aljannah ita ce babbar rabo, rayuwar duniya kuma ba komai ba ce face jin daxi kaxan mai ruxarwa. Allah Maxaukakin sarki ya ce, “Dukkan wata rai za ta xanxani mutuwa, ana cika muku ladanku ne ranar alqiyama, duk wanda aka nesantar da shi daga wuta aka sa shi a Aljannah, to tabbas ya tsira. Rayuwar duniya ba komai ba ce face xan daxi kaxan mai ruxarwa”. (Al-Imran : 185)

Allah ya ce, “ka ce, ni ina tsoron azabar wata rana mai girma in na savawa Ubangijina. Duk wanda aka kawar masa da wannan azabar a wannan ranar to (Allah) ya jiqansa. Wannan shi ne rabo mabayyani”. (Al’an’am : 15 – 16)

Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Lahira ita ta fi alheri kuma ita ta fi wanzuwa”. (Al-aala : 17).



Tags: