Ba a samun kwanciyar hankali sai dai imani da Allah mai girma da buwaya. Duk zuciyar da ba ta da imani za ta zauna cikin tsoro da ruxani da rauni da rashin kwanciyar hankali. Imanin da ake samun tsira da shi shi ne imani da Allah, wanda ma’anarsa shi ne gaskatawa da yankewa cewa Allah shi ne Ubangijin komai, mamallakinsa, mahaliccinsa, kuma Shi kaxai ya cancanta a kaxaita shi da ibada, ta sallah da azumi da addu’a da fata da tsoro da qasqantar da kai, kuma Shi ne ya siffatu da siffofin kamala gaba xaya, ya tsarkaku daga dukkan wani aibi da tawaya, mai girma da buwaya.
Imani da Allah haske ne mai kaiwa zuwa ga adalci, haske ne zuwa ga ‘yanci, haske ne zuwa ga ilimi da sani, haske ne zuwa ga shiriya, haske ne zuwa ga nutsuwa da kwanciyar hankali.Imani da Allah ya qunshi imani da Mala’ikunsa, da littattafansa, da ranar lahira, da imani da qaddara, alkhari ko sharri. Irin wannan imanin shi ne samun arzikin mutum, kai shi ne ma Aljannar duniya ga mumini, wanda qarshensa Aljannar lahira ce Insha Allahu.
IAshar’ance: Shi ne qudurcewa da zuciya, da furtawa da harshe, da aiki da gavvai, yana qaruwa da xa’a ga Allah, yana kuma raguwa da savon Allah.
Idan an gane wannan to a sani tushen karvar ayyuka a wurin Allah shi ne Imani, saboda faxin Allah mai girma da buwaya : “Duk wanda ya yi ayyukan qwarai yana mai imani”. (Al-anbiya’a : 94)
Haqiqa mafi falalar ayyuka da tsarkinsu a wajen Allah shi ne Imani, saboda hadisin da Abu Zarrin – Allah ya yarda da shi – ya tambayi Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Ya Manzon Allah, waxanna ayyuka ne suka fi falala? Sai ya ce, “Imani da Allah da jihadi a kan tafarkinsa” (Muslim ne ya rawaito shi)
Shi ne sababin shiriya da samun arzikin duniya da na lahira, saboda faxin Allah mai girma da buwaya : “Duk wanda Allah ya yi nufin ya shirye shi sai ya yalwata zuciyarsa ga musulunci” (Al-an’am : 125).
Kuma imani yana kawar da mumini daga savon Allah, saboda faxin Allah Ta’ala, “Waxanda suka yi taqawa idan wani mai kewaye daga shaixan ya shafe su sai su tuna Allah, sai ga su suna gani” (Al-aaraf : 201)
Imani sharaxi ne na karvar aiki, Allah yana cewa : “Haqiqa an maka wahayi da waxanda suke gabaninka cewa lallai idan ka yi shirka, to tabbas ayyukanka za su rushe, kuma wallahi za ka zama daga cikin masu hasara” (Azzumar : 65).
Tsarkaken Imani, Allah yana sa albarka a cikin aikin da aka yi a cikinsa, yana karvar addu’o’i da shi, “Haqiqa an maka wahayi da waxanda suke gabaninka cewa lallai idan ka yi shirka, tabbas ayyukanka za su rushe, kuma wallahi za ka zama daga cikin masu hasara” (Azzumar : 65).
Tsarkaken Imani, Allah yana sa albarka a cikin aikin da aka yi a cikinsa, yana karvar addu’o’i da shi.