Fata shi ne : Jin samuwar Allah da falalarsa da rahamarsa, da samun hutu da kwanciyar hankali yayin da aka tsinkayi karamcinsa da kyautarsa, da yarda da hakan. Fata wani abu ne da yake kora zuciya zuwa ga Allah da neman Aljannarsa. Allah mai girma da buwaya ya ce, “Duk wanda ya aikata mummunan aiki ko ya yi zalunci kansa, sannan yana nemi gafarar Allah, to zai samu Allah mai yawan gafara mai yawan jinqai” (Annisa’i : 110)
Fata kala uku ne, guda biyu ababen so ne, guda xaya kuwa ba a son shi.
1-Fata wanda ya yi aiki da xa’ar Allah a bisa hasken Allah yana mai neman lada a wurin Allah.
2-Fatan da wanda ya yi zunubi sannan ya tuba yake yi, yana fatan gafara Allah da shafe zunubbain da yafe masa su da suturta shi.
3-Fata na wanda ya ci gaba da sakaci da savo da munanan ayyuka yake yi, na fatan rahamar Ubangijinsa da gafara amma fa ba tare da ya yi wani aiki ba!!! To wannan fatan ba komai ba ne face ruxi da fatan qarya, ba fatan gaskiya ba, kuma wannan fata ba a son shi har abada, saboda fatan muminai shi ne wanda ya haxe da aiki. Allah ya ce, .. “ Haqiqa waxanda suka yi imani da waxanda suka yi hijira a kan tafarkin Allah, waxannan suna fatan samun rahamar Allah. Allah mai yawan gafara ne mai yawan jin qai” (Albaqra : 218)
Fata yana da matakai da darajoji, suna bambanta daga wani mutum zuwa wani
1-Fatan da yake sanya dagewa wajen yin ibada, ya haifarwa mai yinsa jin daxi yayin da yake ibada, koda kuwa ibadar mai wahala ce, sai riqa jin daxin ne saboda abin da ya nisanta na zunubai da ababen qi.
2-Fatan masu qoqari sosai, wajen barin abin rayukansu da al’adunsu suka saba da su, da barin abin da zai kawar da su daga abin da Ubangijinsu yake nema, wanda zai kaxaita zukatansu ga Allah kaxai.
Wanda duk yake fatan wani abu zai name shi.3-Fatan Ma’abota tsarkakan zukata, shi ne fatan gamuwa da Allah, wanda yake sa su shauqin zuciya da ratayarta ga Allah kaxai. Wannan fatan shi ya fi dukkan sauran nau’o’in fata. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Duk wanda ya kasance yana fatan gamuwa da Uabangijinsa to ya yi aiki na qwarai, kada kuma ya shirka wajen bautawa Ubangijinsa da wani” (Alkahfi : 110)
Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Wanda yake fatan gamuwa da Allah to ajalin da Allah ya sanya mai zuwa ne, kuma shi (Allah) mai ji ne kuma masani” (Al-ankabut : 5)
Mai fata wani mutum ne da yake dauwama akan ayyukan xa’a ga Allah, yana mai tsayuwa da abubuwan da imani ya nuna, yana fata a wurin Allah mai girma da buwaya kada ya karkatar da shi, ya karvi aikinsa kada ya dawo masa da shi, ya ninka masa ladansa, don haka yana qoqarin bin sabubban da suke kawo rahama daidai iyawarsa, yana fatan rahamar Ubangjijinsa, saboda saninsa ga sunayen Allah da siffofinsa, ya riga ya san yana mu’amala ne da Allah mai rahama, mai son bayinsa, mai godiya, mai karamci, mai yawan bayarwa, mai yawan gafara, mai tausayi, don haka a nan duniya yana tsoro, yana kuma fatan aminci idan ya koma zuwa ga Ubangijinsa.
1-Yana qarawa mai yin shi qoqarin dagewa wajen yin ayyuka da xa’a ga Allah.
2-Yana sa mai yin sa ya saba da dauwama akan ayyukan xa’a, a kowane irin halin da ya shiga.
Mai fata koyaushe zai kasance mai kwaxayi a wajen Allah, mai tsoro, mai san falalar Ubangijinsa, mai kyautata zato ga ubangijinsa.3-Yana sa mai yin sa ya saba da dauwama wajen fuskantar Allah, da ganawa da shi, da tausasawa wajen roqonsa tare da naci.
4-Yana fito da bautar bawa ga Ubangijinsa da buqatuwarsa gareshi a fili, tare da jin cewa shi ba zai tava wadatuwa ga barin falalar Allah ba, da kyautatawarsa a kowanne lokaci.
5-Sani da sakankancewa da samuwar Allah da karamcinsa, Allah tsarki ya tabbata a gare shi, shi ne mai yalwar mai bayarwa, don haka yana so bayinsa su yi fata a wajensa, su kuma nace.
Mumini ya kyautata wa Ubangijinsa zato sai ya yi kyakkyawan aiki. Fajiri kuwa ya munanawa Ubangijinsa zato sai ya munana aiki.6-Fata nagari yana kai bawa zuwa ga soyayyar Allah Maxaukakin Sarki da isa zuwa ga qololuwar soyayya, duk lokacin da fatan bawa ga Allah ya qaru, ya kuma samu abin da yake fatan, sai ya qara son Ubangijinsa, ya qara gode masa da yarda da shi, wannan kuwa yana cikin rukunan da bautawa Allah take kawo wa.
7-Yana kai bawa zuwa ga maqamin godiya, domin zai zaburar da shi ganin ya isa zuwa maqamin godiya akan ni’imomi, wannan kuwa ita ce tsantsar bauta ga Allah.
8-Sanin Sunayen Allah da sifofinsa, Shi Allah shi ne mai jinqai, mai karamci, mai yawan bayarwa, mai amsawa wanda ya kira shi, kyakkyawa, mawadaci tsarki ya tabbata a gare shi, babu wanda ya kai girman Allah.
Yana cikin kyautata zato ga Allah ka sani cewa Allah ba ya tozarta wanda ya koma zuwa gare shi.9-Sababi ne na bawa ya samu abin da yake fata, saboda samun abin da ake nema yana taimakawa akan jajircewa da neman qari da fuskantar Allah, hakanan bawa ba zai gushe ba imaninsa yana qaruwa yana qara kusantar Allah mai Rahama.
10-Farin cikin muminai ranar alqiyama da samun abin da suke fata, na yardar Allah da Aljannah, da ganin Allah, duka gwargwadon yadda suke bayi suke fata, da gwargwadon tsoronsu ga Allah a duniya.
1-Tsoron Allah yana lazimta fata gare shi, kamar yadda fata gare shi yana lazimta tsoronsa a wajen mumini, don haka ma yana da kyau samun fata a wurin da yake kyau a samu tsoro.. “Me ya sameku ba ku fatan nutsuwa ga Allah” (Nuhu : 13)
Kuma Allah mai girma da buwaya ya ce, “Ka cewa waxanda suka yi imani su yi gafara ga waxanda ba sa tsoron azabar Ubangiji” (Aljasiya : 14)
Ma’ana basa tsoron abubuwan da Allah zai afko musu kamar yadda suka afkawa waxanda suke gabaninsu na halakarwa da rushewa.
Ba zan so ba a ce babana ne zai min hisabi, domin Ubangijina ya fi min alheri fiye da babana.2-Fata nagari wani magani ne da muke buqatarsa a duk lokacin da
- xebe qauna ya mamaye zukata, suka bar ibada
- tsoro ya rinjayi mutum, har yana cutar da kansa da iyalansa, tsoronsa ya qetare inda shari’a ta ce, to irin wannan yanayi ba makawa sai bawa ya samu abin da zai daidaita tsoronsa, wanda shi ne fata nagari..
Ibada ba ta cika sai da tsoro da fata nagari, da tsoro ake barin abubuwan da aka hana, da kuma fata ne ake yawaita biyayya.3-Fata kishiyar xebe qauna ne, xebe qauna shi ne tunanin rasa rahamar Allah, da barin nemanta, wanda wannan sababin halaka ne da kafirci. Allah ya ce, “kada ku xebe qauna daga rahamar Allah, babu wanda yake xebe qauna daga rahamar Allah sai mutane kafirai”. (Yusuf : 87)