Allah ya ce “”Allah yana da sunaye mafiya kyau ku bauta masa da su. Ku bar waxanda suke karkacewa a cikin sunayensa, za a saka musu abin da suka kasance suna aikatawa” (Al’aaraf : 180)
Sunayen Allah Maxaukakin Sarki dukkaninsu sunaye na yabo, kuma Allah ya siffata su da cewa mafiya kyau ne, ya ce, “Allah yana da sunaye mafiya kyau ku bauta masa da su. Ku bar waxanda suke karkacewa a cikin sunayensa, za a saka musu abin da suka kasance suna aikatawa” (Al-aaraf : 180)
Ba wai kawai suna da kyau ne ba a lafazi, a’a har a cikin abin da suka qunsa na siffofi na kamala. Sunayen Allah gabaxayansu sunaye na yabo da girma, don haka suka zama mafiya kyau, haka ma siffofinsa siffofi ne na kamala, sifofi ne na girma, ayyukansa gabaxaya ayyuka ne na hikima da rahama da maslaha da adalci.
Yana cikin imani, imani da sunayen Allah da siffofinsa, kamar yadda suka zo a cikin littafinsa da sunnar Manzon Allah (S.A.W) ingantacciya, akan qa’idoji guda biyu :
-Qa’ida ta farko :
Tabbatar wa da Allah sunayensa kamar yadda ya dace da girmansa, ba tare da canza ma’ana ba, ko koreta, ko kamantawa, ko misaltawa, don gaskata faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Babu abin da ya yi kama da shi. Shi mai ji ne mai gani” (Asshura : 11)
-Qa’ida ta biyu :
Fahimtar ma’anarsu, da tabbatar da siffofin da suke qunshe da su, ba tare da qoqarin sani yadda siffar take ba. Allah Maxaukakin Sarki ya ce, “Yana sane da abin da yake gabansu da bayansu, su kuma ba sa kewaye shi da sani” (Xaha : 110)
Allah ya bayyana manufar saninsa da sunayensa mafiya kyau, da siffofinsa maxaukaka, shi ne bauta masa da su, kamar yadda ya ce, “Ka ce ku kirawo sunan Allah ko sunan Arrahman, kowanne kuka kirawo to yana da sunaye mafi kyau” (Al-isra’i : 110)
Allah mai girma da buwaya ya ce, “Allah yana da sunaye mafiya kyau ku bauta masa da su. Ku bar waxanda suke karkacewa a cikin sunayensa, za a saka musu abin da suka kasance suna aikatawa” (Al-aaraf : 180)
Kiran Allah da sunayensa mafiya kyau, ya haxa nau’ika biyu na kira, kiran roqo, kamar bawa ya ce, “ya Allah ka ba ni kaza… Ya Mai Rahama ka jiqaina, Ya Mai Karamci ka yi min karamci” da kuma roqo na yabo da bauta, kamar yabon Allah da sunayensa da siffofinsa, ba tare da roqon wani abu ba. Yabon zai iya kasancewa da zuciya ko harshe ga Allah mai girma, ma’abocin sunaye mafiya kyau da siffofi maxaukaka.
Karkacewa cikin sunayen Allah shi ne inkarinsu da qaryata wasu daga cikinsu, waxanda suka zo a cikin littafin Allah mai girma, ko kuma kamanta sunayensa da wani abu daga halittarsa, ko kiransa da siffata shi da abin da bai dace ba, wanda babu wani dalili akan su daga maganar Allah ko sunnar Manzonsa Muhammad (S.A.W)