Mahimmancin Sanin Sunayen Allah Da Siffofinsa

Mahimmancin Sanin Sunayen Allah Da Siffofinsa

Mahimmancin Sanin Sunayen Allah Da Siffofinsa

Mahimmanci sanin sunayen Allah da Siffofinsa yana bayyana ta abubuwa kamar haka:

Na farko : Mafi girman ilimi shi ne ilimin da yake da alaqa da Allah da sunayensa mafiya kyau, da siffofinsa maxaukaka, gwargwadon yadda bawa ya san

Sunayen Allah da siffofinsa gwargwadon yadda zai zama yana da rabo daga bautar Allah, da samun nutsuwa da shi da son shi da girmama shi, wanda wannan zai sa shi neman rabauta da yardar Allah da Aljannarsa, da samun ni’imar ganinsa a lahira. Wannan kuwa wata manufa ce da bata samuwa sai da dace daga wajen Allah mai girma da buwaya.

Na biyu : Sanin sunayen Allah da siffofinsa shi ne tushen ilimi da ginshiqin imani, kuma farkon wajibai, idan mutane suka san Ubangijinsu sai su bauta masa iyakar bauta, Allah ya ce, “Ka sani cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah” (Muhammad : 19)

Darajar Ilimi tana bayyana daga darajar abin da ilimin yake koyarwa, babu wani ilimi da ya fi ilimin sanin Allah da siffofinsa daraja

Na uku : Cikin sanin sunayen Allah da siffofinsa akwai samun qaruwar imani da yaqini, da tabbatar da tauhidi, da xanxanar zaqin bauta, kuma wannan shi ne ruhin imani da asalinsa da tuqewarsa. Hanya ta kusa zuwa ga wannan kuwa ita ce lura da bibiyar siffofin Allah da sunayensa daga Alqur’ani, saboda Allah mai girma da buwaya idan yana son ya girmama bawa da saninsa, kuma ya tara zuciyarsa a kan son shi, sai ya yalwata masa qirjinsa ya karanci siffofinsa, daga Alqur’ani. Idan wata siffa ta zo daga wahayi sai ta karve ta, ya yarda da ita, ya sallama, ya miqa wuya ya bi, zuciyarsa ta yi haske.

Qirjinsa ya yalwatu gare shi, ya cika da farin ciki da qauna, farin cikinsa ya tsananta, ya wadatu sosai, iliminsa ya yi qarfi, hankalinsa ya kwanta, zuciyarsa ta samu nutsuwa, ya kewaya cikin lambun ilimi, basirarsa ta shaqi qanshin wannan lambu, saboda sakankancewarsa cewa darajar ilimi tana bin darajar abin da yake koyarwa. Babu kuwa wani abin da ake koyo da yafi girma, yafi falala fiye da ilimin da yake da wannan siffa. Allah ma’abocin sunaye ne mafiya kyau, da siffofi maxaukaki, shi ma darajarsa gwargwadon yadda ake buqatarsa, babu wani abu da zukata suke da buqata fiye da sani mahaliccinsu, da son shi, da farin ciki da shi, da neman kusantar shi. Babu wata hanya ta sanin haka sai ta hanyar sanin siffofinsa da sunayensa, duk lokacin da bawa ya fi sanin sunayen Allah da siffofinsa to yafi sanin Allah, kuma ya fi neman shi, da kusanci da shi, a duk lokacin da bawa yafi kowa inkarin siffofin Allah to ya fi kowa jahilci, da qin Allah, da nisa da shi. Allah ya baiwa bawa matsayi irin matsayin da bawa ya baiwa Allah a wajensa.

Na huxu : Haqiqanin wanda ya san Allah yana kafa hujja ne da abin da ya sani na sunayensa da siffofinsa a kan abin da yake aikatawa ko yake shar’antawa na shari’o’I, saboda Allah Maxaukakin Sarki ba ya aikata komai sai abin da sunayensa da siffofinsa suka nuna. Ayyukan Allah suna kewayawa ne tsakanin adalci da falala. Haka nan Allah ba ya shar’anta hukunce-hukunce sai abin da hikimarsa da falalarsa da adalcinsa suka nuna, duka labaran Allah gaskiya ne, duka umarnin Allah da haninsa adalci ne da hikima da rahama. Wannan kuwa wani ilimi ne da bayyanarsa ta fi qarfin a yi bayaninta.

Sanin Allah da sunayensa da siffofinsa shi ne gyaruwar zuciya da cikar imani.

Na biyar : Alaqa mai qarfi tsakanin siffofin Allah mai girma da buwaya da abin da ya hukunta na ibadu a fili da voye, domin kowacce siffa a qarqashinta akwai wata kevantacciyar bauta, haka abin yake a dukkan nau’o’in ibadu na zuciya da na gavvai, bawa ya san Allah ya kaxaita da cutarwa da amfanarwa, da bayarwa da hanawa, da halitta, da azurtawa, da rayawa da kashewa, wannan zai haifar masa da bautar dogaro ga Allah a voye, da abin da kuma dogaro ga Allah ya qunsa a fili. Sanin da bawa ya yi na cewa Allah yana ji, yana gani, babu wani abu daidai da qwayar zarra da yake vuya gare shi, ya san abin da yake voye da wanda yake sarari, ya san abin da idanu maha’inta suke yi, kuma ya san abin da zukata suka voye, wannan zai sa bawa ya kiyaye harshensa da gavvansa da waswasinsa, zai yi qoqari ya kiyaye su daga abin da Allah bai yarda da shi ba, ya kuma sanya waxannan gavvai akan abin da Allah yake so, ya kuma yarda da shi, ya samu kunya a voye, da kunyar nisantar haramun da munanan ayyuka. Sanin bawa da wadatar Allah da karamcinsa, da kyautatawarsa da rahamarsa, yana qara wa bawa fata mai yawa a wurin Allah. Hakanan sanin bawa da girman Allah da xaukakarsa da buwayarsa, yana haifar masa da qasqantar da kai da son Allah, waxannan halaye kuma sai su haifar masa da nau’oin ibada na fili, don haka duk bauta ta koma zuwa ga sunayen Allah da siffofinsa.

Na shida : Bauta da sunayen Allah da siffofinsa tana da tasirin mai kyau akan gyaruwa zuciya, da gyaruwar halaye, kamar yadda watsi da hakan ya kan jawo cuttuttukan zuciya

Na bakwai : Akwai lallashi a cikin sani sunayen Allah da siffofinsa ga bawa a lokacin da masifu da abubuwan qi suka same shi, saboda idan bawa ya san Ubangijinsa masani ne, mai hikima, mai adalci, ba ya zaluntar kowa, sai bawa ya yarda da abin da ya same shi ya yi haquri, ya gane cewa abubuwan qi da suka same shi da musifu akwai wata maslaha a ciki da amfani, wanda shi bai sani ba, amma haka Allah ya tsara a bisa iliminsa da hikimarsa, sai ya samu nutsuwa da Ubangijinsa, ya maida lamarinsa zuwa gare shi.

Na takwas : Fahimtar ma’anonin sunayen Allah mai girma da buwaya da siffofinsa hanya ce zuwa ga samun son Allah da girmama shi, da fata gare shi, da tsoron shi, da kula da shi, da sauran abubuwan da sanin Allah da sunayensa da siffofinsa suke kawowa.

Na tara : Cikin lura da ma’anonin sunayen Allah da siffofinsa akwai samun taimako akan fahimtar littafin Allah, saboda Allah ya umarce mu da lura da fahimtar Alqur’ani, a inda ya ce, “Littafi ne mai albarka mun saukar da shi don su fahimci ayoyinsa, kuma masu hankali su wa’azantu” (Saad : 29)

Duba da cewa Alqur’ani mai girma cike yake da sunayen Allah da siffofinsa, don haka fahimtarsu qofa ce babba ta fahimtar Alqur’ani, idan ka bibiyi Alqur’ani zaka fahimci cewa akwai wani mai mulki wanda yake tsaye akan dukkan komai, a saman al’arshi, yana jujjuya al’amuran bayinsa, yana umarni ya hanawa, yana aiko da Manzanni, yana saukar da littattafai, yana yarda, yana fushi, yana bada lada, yana uquba, yana bayarwa, yana hanawa, yana xaukakawa, yana qasqantawa, yan xagawa, yana saukewa, yana gani yana ji, daga saman sammai bakwai, ya san abin da yake voye, da na fili, yana aikata abin da ya so, ya siffatu da dukkan kamala, ya kuvuta daga dukkan aibi, babu wani abu da zai motsa sai da izininsa, babu wani ganye da zai faxo sai da saninsa, shi mai hikima ne masani.

Wanda ya samu Allah, to me ya rasa! Wanda kuma ya rasa Allah, to me kuma ya samu!?.

Na goma : Sanin sunayen Allah da siffofinsa yana dasa ladabi ga Allah a cikin zuciya, da jin kunyar Allah. Ladabi ga Allah shi ne tsayawa da yin addininsa, da ladabtuwa da ladubbansa a fili da voye, babu wanda zai zama mai ladabi ga Allah sai ya kiyaye abubuwa uku : sanin Allah da sunayensa da siffofinsa, sanin addininsa da shari’o’insa, da abin da yake so, da abin da baya so, sannan da zuciyar da take shirye wajen karvar gaskiya a ilmance da aiki da hali.

Na sha xaya : Sanin Allah da sunayensa da siffofinsa suna baiwa bawa basirar gane laifukansa da aibobin kansa, sai ya yi qoqarin gyarawa, abubuwan da suke kawo jayayya da musu da gaskiya, guda huxu : girman kai, hassada, fushi, shahara. Abin da kuma yake kawo waxannan huxun shi ne bawa ya jahilci Ubangjijinsa da ya jahilci kansa. Da bawan ya san Ubangijinsa ya san siffofinsa na kamala da xaukaka, ya kuma gane laifukan kansa da matsalolinsa to ba zai yi girman kai ba, kuma ba zai yi fushi ba, kuma ba zai yi wa wani hasada ba a kan abin da Allah ya bashi.

Na sha biyu : Jahiltar sunayen Allah da siffofinsa da rashin fahimtarsu, da bautawa Allah da su, dalili ne na vata da jahilci da halaka, wanda duk bai san Allah da Manzanninsa ba to me ya sani? Kuma wane abu ya gane wanda bai gane wannan ba?. Wane aiki ko ilimi ya samu wanda ilimin sanin Allah da aiki da yardarsa ya wuce shi?. kuma meye da shi. Domin rayuwar xan adam tana tare da rayuwar zuciyarsa da ruhinsa, babu wata rayuwa ga zuciya sai idan ta san wanda ya halicceta, tare da son shi, da bauta masa shi kaxai, da komawa zuwa gare shi, duk wanda ya rasa wannan rayuwa to ya rasa dukkan alheri gabaxaya, koda kuwa ya samu duniya a maimakonta.

Sanin Allah (S.W.T) gyaruwar zukata ne da jiki

Na sha uku : Sanin sunayen Allah da siffofinsa sababi ne na tsantsanta tauhidi, da samun cikar imani, kuma ayyukan zuciya su bayyana, na tsarkake ibada, da so, da tsoro, da fata, da dogara ga Allah shi kaxai. Duk da girman wannan babi wajen gyara zukata da tace su, da raba su da waswasin shaixan, kaxan ne cikin mutane masu kula da shi. Duk wanda kuwa ya lura da shari’a da madogararta, sai ta fahimci alaqar ayyukan gavvai da ayyukan zukata, kuma ayyukan gavvai ba sa amfani in babu na zukata, kuma ayyukan zukata sun fi zama wajibi fiye da na gavvai. Shin mumini yana bambanta da munafiki ne in ba don abin da yake zuciya ba na aikin da kowa yake yi, wanda yake bambanta su, shin akwai wanda zai iya shiga musulunci ba tare da aikin zuciya ba kafin gavvansa su yi. Don haka bautar zuciya ta fi bautar gavvai, kuma ta fi yawa da dauwama, kuma ita ce hanya zuwa ga bautar gavvai, don haka wajiba ce a kowanne lokaci.



Tags: