Sanin sunayen Allah mafiya kyau, da siffofinsa maxaukaka yana daga cikin mafi mafi darajar ilimi, kowane suna daga cikin sunayensa yana da wata siffa da ya kevanta da ita. Dukkan sunayen Allah siffofi ne na yabo da kamala, kowa ce siffa kuma tana da abin da take hunkuntawa da nunawa. Don haka ba zai yi wu ba a raba zatin Allah da sunayensa, ko a raba sunayensa da ma’anoninsu da siffofinsu. Ko a kore abin da siffofinsa suka nuna na ayyuka da tasiri. Duk wannan yana cikin tasirin sunayen Allah da sifofinsa.
Duk ayyukan Allah qunshe suke da hikima da maslaha. Sunayensa duka mafiya kyau ne. Ba zai taba yiwu wa ba a ce ba su da wata ma’ana a cikinsu. Dan haka Allah Ta’ala ya yi inkari ga wanda ya kore wa Allah umarninsa da haninsa, ko ya kore masa sakamakon da uqubarsa, ya nuna ya danganta shi zuwa ga abin da bai dace da shi ba, da abin da ya tsarkaka daga barinsa, kuma wannan mummunan hukunci ne ga wanda ya yi hukunci da shi, duk kuma wanda ya danganta shi zuwa ga haka, to bai girmama shi ba yadda ya dace ya girmama shi, kamar yadda Allah ya ce ga masu inkarin Annabta da aiko da Manzanni da saukar da littattafai, ya ce, “Ba su girmama Allah ba iyakar girmamawa, yayin da suka ce Allah bai saukar da wani abu ba ga wani mutum” (Al’an’am : 91)
Allah ya ce dangane da waxanda suke inkarin ranar qiyama da sakamako da uquba, ya ce, “Ba su gimama Allah ba, yadda ya kamata su girmama shi, alhali qasa gabaxayanta damqarsa a ranar alqiyama, sammai kuma suna naxe a damansa” (Azzumar : 67)
Dangane da waxanda suka ce Allah zai daidaita tsakanin abubuwan da suka sava da juna, kamar masu biyayya da masu fajirci, ko muminai da kafirai, Allah ya ce : “Waxanda suka yi munanan ayyuka suna zaton za mu sanya su kamar waxanda suka yi imani kuma suka yi ayyuka na qwarai, daidai ne mutuwarsu da rayuwarsu, abin da suke hukuntawa ya yi muni” (al-jaasiya : 21)
Allah ya ba da labarin cewa hukuncinsu mummuna ne, sunayen Allah da siffofinsa ba za su xauki haka ba,
Allah ya ce, “Yanzu kuna zaton mun halicce ku don wasa ne, kuma ba za ku dawo wajenmu ba. To Allah ya xaukaka sarki na gaskiya, wanda babu wani abin bautawa da gaskiya sai shi, Ubangijin Al’arshi mai girma” (Almuminuna : 115 – 116)
Allah ya xaukaka daga zaton masu mummunan zato, wanda sunayen Allah da siffofinsa ba za su xauke shi ba.
Irin wannan yana nan da yawa a cikin Alqur’ani. Allah yana korewa kansa savanin abin da sunayensa da siffofinsa suka nuna, domin hakan yana rushe kamalar su ne da ma’anoninsu.
Sunan shi na (Abin yabo mai girma) yana hana barin mutum kara-zube ba tare da wani aiki ba, ba umarni ba hani, ba lada ba azaba. Kamar yadda sunan shi “Mai hikima” shi ma yana nuna haka, haka ma sunanshi na “Mai mulki”
Sunan Allah “Rayayye” yana kore a ce Allah ba ya wani aiki, saboda haqiqanin rayuwa shi ne aiki, saboda duk wani rayayye to mai yawan aiki ne. Kasancewarsa mai halitta, wanda yake tsaye da zatinsa, yana nuna rayuwarsa. Sunan Allah “Mai ji mai gani” yana nuna akwai abin da ake ji, kuma ake gani. Sunan Allah (Mai halitta) yana nuna akwai halitta, haka nan sunan (Mai azurtawa) da (Mai mulki) yana nuna abin da aka mallaka, da tasarrufi, da tsarawa, da bayarwa, da hanawa, da adalci, da ba da lada, da yin uquba. Sunayen Allah “Mai alheri, Mai kyautatawa, mai bayarwa mai yawan kyauta” da sauransu duk suna nuna ayyuka da tasirinsu.
Sunayen Allah (Mai yawan gafara, Mai karvan tuba, mai afuwa” ba makawa sun ratayu da wani abu, domin ba makawa a samu laifin da za a gafarta, da tuban da za a karva, da laifukan da za a yi wa afuwa. Ba makawa sunan “Mai hikima” a samu inda hikimar za ta bayyana, abin da waxannan sunaye suke nunawa kamar abin da sunayen Allah na Mai halitta da Azurtawa da bayarwa da hanawa suke nunawa, na wanda aka halitta, da wanda aka azurta, da wanda aka ba, da wanda akan hana, dukkansu waxanna sunaye mafiya kyau.
Ubangiji Ta’ala yana son zatinsa da siffofinsa da sunayensa, mai afuwa ne yana son afuwa, yana son gafara, yana son tuba, yana farin ciki da tuban bawansa yayin da ya tuba, farin cikin da bawa ba ya tunaninsa, yana haquri da shi, yana karvar tubansa ya yafe masa.
Allah shi ne “Sha yabo, Mai girma” wannan yabo da godiyar sun hukuntar samar da tasirinsu, daga cikin tasirinsu gafarta kurakurai, da yafewa, da afuwa a kan munanan ayyuka, da yafiya akan laifuffuka, duk da cikakken ikon Allah a kan rama haqqi, da yadda Ubangiji ya san laifukan da aka yi da gwargwadonsu, da yadda ya kamata a yi uquba. Don haka haqurin Allah yana zuwa bayan saninsa, afuwarsa kuma tana kasancewa bayan ikonsa. Gafararsa bayan cikar izzarsa da hikimarsa, kamar yadda ya faxa a kan harshen Almasihu (A.S) ya ce, “In ka azabtar da su, su bayinka ne, in ka yi musu gafara, to kai mabuwayi ne mai gafara” (Alma’idah : 118)
Ma’ana gafararka tana tare da cikakken ikonka da hikimarka, ba kamar wanda yake gafara ba don gazawa, yake yafiya don bai san iya haqqinsa ba, a’a kai Allah ka san haqqinka, kuma za ka iya karvo shi, kuma kana da hikima wajen kavar shi.
Duk wanda ya lura da yadda tasirin sunayen Allah da siffonsa suke gudana a duniya da cikin al’amura, to zai bayyana gare shi cewa tushen hukunta waxannan laifuka na bayi, da qaddara su, yana cikin cikar sunanyen Allah da sifofinsa da ayykansa, kuma babbar abin da suke kaiwa gare shi shi ne gode masa da yabonsa, kamar yadda suke tabbatar da kaxaitakarsa a cikin ayyukansa da bautarsa.
Yana da cikakkiyar hikima cikin duk abin da ya hukunta ya qaddara, akwai kuma ayoyi masu kyau, da kaiwa ga bauta masa da sunayensa da siffofinta, soyayyarsu ga Allah, da gode masa, da bauta masa da sunayensa kyawawa, domin kowanne suna yana da bautarsa da ilimin da halin da ya kevanta da shi. Mafi cikar mutane wajen bautawa Allah shi ne mai bautawa Allah da dukkan sunayensa da sifofinsa, waxanda xan adam ya sani. Yin bauta da wani suna, ba zai hana shi yin bauta ba da wanin sunan, ba zai zama kamar wanda bautawa Allah da sunansa “Mai iko” zai hana shi bauta masa da sunan shi “Mai haquri” ko “mai jinqai, ko bauta da sunansa “mai bayarwa” ya hana shi bauta da suna “mai hanawa” ko bauta da sunanshi “mai jinqai” ko “mai afuwa” ko “mai gafara” ya hana shi bauta da sunanshi mai “Damqa” da makamancin haka.
Bai yi kama da wani abu ba daga cikin halittarsa, kuma babu abin da ya yi kama da shi, bai gushe ba, yana nan da sunayensa da siffofinsa.Allah ya ce, “Allah yana da sunaye mafiya kyau, ku kira shi da su” (Al-aaraf : 180)
Kiransa da su, ya haxa kira na roqo, da kira na yabo, da kira na bauta. Shi Allah (S.W.T) yana kiran bayinsa su san shi da sunayensa da siffofinsa, su yabe shi da su, su kuma samu rabonsa na bautawa musu da su.
Allah yana son abin da sunayensa suke nunawa. Shi Allah masani ne kuma yana son masani, mai kyauta ne kuma yana son mai kyauta, shi Mara ne (Tilo) kuma yana son mara, mai kyau ne, kuma yana son kyau, mai afuwa ne, kuma yana son afuwa, mai kunya ne, kuma yana son kunya da masu ita, mai xa’a ne kuma yana son masu xa’a, mai godiya ne, kuma yana son masu godiya, mai haquri ne, kuma yana son masu haquri, mai rangwame ne, kuma yana son masu rangwame, saboda yadda Allah yake son tuba da gafara da afuwa da kawar da kai, sai ya haliccin waxanda zai karvi tubansu, ya yi musu afuwa, ya qyale su.