Allah Mai girma da buwaya yana cewa, “Ashe ba ka ga yadda Allah ya buga misalin kalma mai daxi ba, kamar bishiya ce mai daxi da tushenta yana qasa, rassanta kuma suna sama, tana bayar da abincinta a kowanne lokaci da izinin Ubangijinta” (Ibrahim : 24 – 25).
Yana daga cikin fa’idojin imani abin da zai zo :
1-Imani na gaskiya yana sanya nutsuwa da kwanciyar hankali da yalwar qirji, kamar yadda Allah ya ce, “Ku saurara, waliyyan Allah babu tsoro a kansu, kuma babu baqin ciki a tare da su” (Yunus : 62)
2-Samun kevantacciyar kasancewa tare da Allah, wadda yake wa muminai, ma’ana yana fitar da su daga duhun kafirci da wahalhalunsa zuwa ga hasken imani da sakamakonsa.
3-Rabauta da yardar Allah da samun Aljannah, wadda ya tanade ta ga wanda ya yi imani ya gaskata shi. Allah Ta’ala ya ce,“Alqawarin da Allah ya yi wa muminai maza da mata shi ne Aljannatai waxanda qoramu suke gudana a qarqashinsu, da wuraren zama masu daxi a cikin Aljannar zama da samun yardar Allah” (Attauba : 72)
Imani da Allah alaqa ce tsakanin bawa mai rauni da Ubangijinsa, kamar yadda mai qarfi shi ma yake samun qarfinsa.4-Samun kariyar Allah da yake bawa waliyyansa da masoyansa muminai : “Haqiqa Allah yana kare waxanda suka yi imani” (Al-hajj : 38)
Misalin haka : Kariyar da Allah ya bawa Annabinsa Muhammad (S.A.W) a lokacin hijirarsa, da kariyar da ya ba wa Badaxayinsa Ibrahim (S.A.W) lokacin da aka jefa shi cikin wuta.
5-Samun xaukaka a addini da samun jagoranci a cikinsa, Allah yana cewa, “Muka sanya su jagorori suna shiryuwa da umarninmu yayin da suka yi haquri” (Assajdah : 24)
Babban abin da yake nuna haka, jagorancin masu addini da yaqini, Allah ya tabbatar da ambatonsu, ya tabbatar da abin da suka bari a baya, alhali suna qarqashin qasa a binne, jikkunansu basa nan, amma gurabunsu da labarukansu suna nan a raye.
Rayuwar da ba imani mutuwa ce tabbatacciya. Kwayar idon da ba imani makanta ce. Harshen da Imani bebe ne. Hannun da ba imani shanyayye ne.6-Samun Son da Allah yake wa Muminai. Allah Ta’ala ya ce dangane da muminai, “Yana son su, suna son shi” (Al-ma’idah : 54).
Kuma Ya ce, “Waxanda suka yi imani da ayyuka na qwarai Allah mai rahama zai sanya qaunarsu da son su (a zukatan bayinsa) (Maryam : 96).
7-Samun rayuwa mai daxi duniya da lahira. Allah ya ce, “Wanda duk ya yi aiki na qwarai namiji ko mace, alhali yana mumini, to za mu raya shi rayuwa mai daxi, kuma tabbas wallahi za mu saka masa ladansa da mafi kyan abin da suke aikatawa” (Annahli : 97).
To ina masu neman rayuwa mai daxi da kwanciyar hankali da arziki?!!
8-Samun son da Allah yake wa mumini, da son mumini da yake wa Allah, Allah yana cewa, “(Allah) yana son su, kuma suma son shi” (Al’ma’idah 54)
Ma’ana, yana son su, kuma ya sanya son su da qaunarsu a tsakanin mutane.
9-Samun Busharar da aka yi wa masu imani ta girmamawar Allah gare su, Allah yana cewa, “Ka yi wa muminai bushara” (Attaubah : 112).
Bushara kuwa ba ta kasancewa sai da wani abu mai girma, wanda in aka faxe shi sai ka ga alamunta a a fatar wanda aka faxa masa ita, don haka ma ake ce mata bushara. Babu wata bushara da tafi rahamar Allah da yardarsa da Aljannarsa girma. Allah yana cewa, “Ka yi wa waxanda suka yi imani, kuma suka yi ayyukan qwarai albishir cewa suna da Aljannatai waxanda qoramu suke gudana a qarqashinsu” (Albaqrah : 25)
10-Imani sababi ne na samun tabbata, Allah yana cewa, “Waxanda mutane suka ce musu : “Lallai mutane sun yi muku taron dangi, ku ji tsoronsu” Sai hakan ya qara musu imani, suka ce, Allah ya isar mana, kuma madallah da abin dogaro” (Ali- Imran : 173).
Babu abin da ya fi nuna irin wannan tabbatar, fiye da abin da tarihi ya rubuta na yadda Annabawa da Sahabbai da Tabi’ai da waxanda suka biyo bayansu suka yi sadaukarwa ga addini.
11-Amfanuwa da wa’azi, Allah yana cewa, “Ka tunatar, haqiqa tunatarwa tana amfanar muminai” (Azzariyat : 55)
Ba wanda yake amfanuwa da tunatarwa da wa’azi sai masu imani.
12-Samun kai cikin alheri a kowanne hali, a halin qunci ko yalwa, shi dai mumini yana tare da alheri. Manzon Allah ya ce, “Abin mamakin al’amarin mumini, shi ne dukkan al’amuransa alheri ne, babu wanda yake da haka sai mumini, idan abin farin ciki ya same shi, sai ya gode, sai ya zamar masa alheri, idan kuma cuta ta same shi, sai ya yi haquri, sai ya zamar masa alheri” (Muslim ne ya rawaito shi”.
Imani yana sanya mai shi haquri akan cuta, da godiya akan abin farin ciki.
13-Samun kariya daga faxawa cikin manya – manyan zunubai, ya inganta daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Mazinaci ba ya zina a lokacin da yake yi yana mumini” (Bukhari ne ya rawaito).
Waxannan su ne manya – manayan fa’idojin imani, to ina masu neman kwanciyar hankali da nutsuwa?!.
Yana daga cikin Alamomin imani a rayuwar mumini :
1-qaruwar kwaxayin mumini wajen miqa wuya da jayuwa ga shari’a, Allah yana cewa, “Kaxai abin da muminai suke faxa idan an kirawo su zuwa ga Allah da Manzonsa don yin hukunci tsakaninsu shi ne su ce, mun ji mun bi, waxannan su ne masu rabauta”.(Annur : 51)
Imani yana sanya ma’abocinsa yin gaggawa zuwa ga kamanta da bin umarnin Allah mai girma da buwaya
Allah Ta’ala yana cewa “Na rantse da Ubangijinka ba za su yi imani ba, har sun hukunta ka akan abin da ya faru tsakaninsu, sannan kuma baza su ji qunci ko damuwa ba dangane da abin da ka hunkunta, su kuma sallama, sallamawa ta gabaxaya” (Annisa’i : 65)
Kai Imani yana sanya ma’abocinsa ya sallamawa da yarda da lamarin Allah mai girma da buwaya
Imani da Allah shi ne rayuwa, kuma rayuwa tare da Allah ita ce imani2-Kariyar Allah ga bawansa da shirka boyayya da bayananniya, kamar qin juyar da wani abu na addu’a ko neman taimako da agaji ga wanin Allah mai girma da buwaya, domin mai amfanarwa shi ne Allah, haka ma mai cutarwa shi ne Allah mai girma da buwaya “Idan Allah ya shafe ka da wata cuta to babu mai yayewata sai shi” (Al-an’am : 17)
3-So don Allah da qi don Allah, wannan kuwa shi ne mafi qarfin igiyar imani, Allah yana cewa : “Muminai yan uwan juna ne” (Al-hujurat : 10)
4-Babu abin da yake nuna haka fiye da yan uwantakar sahabban Madina ga yan uwansu sahabban da suka yi hijira daga Makkah (Almuhajiruun), da yadda suka ba da kawunansu da dukiyoyinsu ga yan uwansu, Manzon Allah ya ce, “Xayanku ba zai yi imani ba, har sai ya so wa xan uwansa abin da yake so wa kansa” (Bukhari ne ya rawaito shi)
5-Haquri a wajen Jihadi akan tafarkin Allah, da bayar da abu mai tsada da qima don yardar Allah, Allah yana cewa, “Muminai su ne waxanda suke yi imani da Allah da Manzonsa, sannan ba su yi shakka ba, suka yi jihadi da dukiyoyinsu da rayukansu saboda Allah, waxannan su ne masu gaskiya” (Alhujurat : 15)
6-Rataya zuciya ga Allah da alqawarinsa, da abin da yake wajensa, da jin daxin hakan, Aljannar duniya a wajen mumini ita ce imani da bin Allah mai rahama, don haka yana fatan samun Aljannar lahira, wadda ita ce Allah ya yi masa alqawari, kuma yana san ran samun lada daga wajen Allah akan dukkan abin da ya same shi na wahala da gajiya, a rubuta masa a cikin takardun ayyukansa. Allah yana cewa “Baya halatta ga mutanen Madinah da larabawan da suke kewayansu su qi bin Manzon Allah (Wajen yaqi), ko su so rayukansu akan ran (Manzon Allah) domin kuwa babu wata ishirwa ko wahala ko yunwa da za ta same su saboda Allah, ko su taka wani wuri da zai baqantawa kafirai rai, haka nan ba su yiwa kafitai wani abu ba face sai an rubuta musu kyakkyawan aiki akan hakan. Haqiqa Allah ba ya tozarta aikin masu kyautatawa. Haka nan ba za su ciyar da wata ciyarwa ba, babba ko qarama, ba za su shiga wani kwari ba, face an rubuta musu (ladan wannan aiki) don Allah ya saka musu da mafi kyan abin da suke aikatawa” (Attaubah : 120 – 121)
“Ya ku waxanda suka yi imani ku yi imani”. Ya kira su da sunan imani, ya kuma kwaxaitar da su a kanshi, don saboda matsayin imaninDukkan waxannan suna faruwa ne ga waxanda suka yi imani da Allah, da gaskiya cikin mu’amala.
7-Samun Jivintar Allah da Manzonsa (walittaka). Allah mai girma da buwaya ya ce, “Kaxai macivinci lamarinku shi ne Allah da Manzonsa da waxanda suke yi imani” (Alma’idah : 55)
Jibintar Allah tana nufin son da Allah, da taimakon addininsa, da son waliyyansa, da barranta daga kishiyar haka, waxanda su ne maqiya Allah, Allah yana cewa, “Ba za ka samu mutanen da suka yi imani da Allah da ranar lahira suna son waxanda suka savawa Allah da Manzonsa koda kuwa iyayensu ne ko yayansu ko yan uwansu ko danginsu, waxannan su ne waxanda Allah ya rubuta musu imani a cikin zukatansu, ya kuma qarfafa su da ruhi daga wajensa, kuma yana shigar da su Aljanatai waxanda qoramu suke gudana ta qarqashin su, suna masu dawwama a cikinsu, Allah ya yarda da su, suma sun yarda da shi. Ku saurara rundunan Allah su ne masu rabauta” (Almujadala : 22)
Mumini yana son Allah da manzonsa da muminai, ba ya kuma riqon kafirai masoya. Allah yana cewa, “Kada muminai su riqi kafirai masoya koma bayan Muminai” (Ali- Imran : 28)
8-Samun kyawawan halaye. Ya tabbata Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Kunya da imani an haxa su waje xaya, idan aka xauke xaya, to sai xayan ma sai ya tafi” (Baihaqi ya rawaito shi)
Xabi’ar kunya tana daga cikin manya-manyan halaye, mumini yana kyautata halayensa tare yan uwansa, don ya rayu a cikin ni’imar duniya ba tare da wasu matsaloli ba ko rarrabuwa ko husuma, duk wannan suna samuwa ne saboda shi mumini, don haka ba wanda yake samun haka sai mumini.
9-Samun haqiqanin arziki da kwanciyar hankali, shi ne abin da yake sawa mumini jin cewa yana Aljannar duniya, saboda arziqi da kwanciyar hankali, saboda yana da Ubangiji xaya, Annabi xaya, shi ne Muhmammad xan Abdullahi (S.A.W), da kuma tsari xaya, shi ne bin yardar Allah, da kuma manufa xaya, wadda ita ce Aljannah, da faxinta faxin sammai da qassai ne.
Idan ka duba dama da hagu za ka ga asibitoci da wuraren duba tavin hankali sun cika da marasa lafiya, zaka kuma ji koke – koken da damuwa da rashin barci da abubuwan ban tsoro kala-kala, sai ka gane cewa dukkan waxannan abubuwa abin da ya kawo su shi ne nisantar imani da Allah mai girma da buwaya, da karkata ga duniya da xamfaruwa da ita, har ya zamana son duniya ya mamaye kula da gyara zuciya, shi ko xan adam yana da tsananin buqatar ciyar da zuciyarsa abincinta, wanda shi ne Imani da Allah da komawa zuwa gare shi, da dauwama wajen ambatonsa, da imani da mala’iku da littattafai, da ranar lahira, da qaddara alherinta ko sharrinta, mai xaxi ko maras daxi, duk a yi imani daga Allah take.
A taqaice dai da yawa daga cikin mutane sun gafala daga maganin zuciya, da samun hutunta, da barin Aljannar duniya, sun koma bayan tarkacen duniya mai qarewa, don haka su ba su samu abin da suke nema ba, kuma ba su huta ba tun daga farko.
Qosar da bangaren ruhi ba ya samuwa sai da imani, saboda ruhi daga Allah yake, Allah ne ya halicce shi, jiki kuma Allah ya halicce shi ne daga qasa, don haka duk lokacin da xan adam ya qosar da bangaren ruhinsa sai ya ruhinsa ya xaukaka, ya yi sama, ya nisanci qananan al’amura ta samu nutsuwa, amma duk lokacin da ya yi watsi da wannan vangaren, sai ruhinsa ya yo qasa zuwa ga xabi’ar dabbobi ta sha’awa, quncin rai da damuwa su qaru, duniya ta yi mata baqinqirin.